Siyasar Katsina ta dauki sabon salo

Ga duk mai bibiyar siyasar Jihar Katsina, ya gani ko ya ji yadda siyasar ta dauko wani irin salo, mai matukar sosa zukatan jama’a. Hakika siyasa rigar ’yanci a tun lokacin da shugaban hukumar zabe ta Najeriya, Malam Attahiru Jega ya buga gangar siyasa, Makada da masu rawa suka bazama wajen kida da taka rawarsu […]

Siyasar Katsina ta dauki sabon salo
Siyasar Katsina ta dauki sabon salo

Ga duk mai bibiyar siyasar Jihar Katsina, ya gani ko ya ji yadda siyasar ta dauko wani irin salo, mai matukar sosa zukatan jama’a. Hakika siyasa rigar ’yanci a tun lokacin da shugaban hukumar zabe ta Najeriya, Malam Attahiru Jega ya buga gangar siyasa, Makada da masu rawa suka bazama wajen kida da taka rawarsu a sassan kasar nan. Haka su ma ’yan siyasar Jihar Katsina ba a barsu a baya ba wajen taka rawar.Tabbas siyasar Jihar Katsina siyasa ce wadda take matukar daukar hankalin jama’a, tun daga al’ummar Jihar Katsina da na kasar mu Najeriya kai har ma zuwa wasu kasashen waje, A zaben da ya gabata na 2011. 

A wancan lokaci gwamnan mai ci a halin yanzu, wato Lauya Ibrahim Shehu Shema ya fafata takarar sa ne da Sanata Yakubu Lado danmarke na jam’iyyar C.P.C, inda wannnan fafatawa ta ja hankalin dimbin jama’a, inda har wasu manazarta lamurran siyasa suke cewa Gwamna Ibrahim Shehu Shema ya sha da kyar wajen komawar sa akan kujera, domin bai ji da dadi ba a fafatawar da suka yi da abokin hamayyarsa na jam’iyyar adawa ta C.P.C.
To, ga dukkan alamu a wannan siyasar ta bana, wadda ake cikin taka rawar ta, tare da tallata hajoji da ’yan’siyasar ke yi, siyasar tana dauke da wani sabon salo, wanda wasu manazarta lamurran siyasar ke hasashen sai ya dara na 2011. Domin ’yan takarar kujerar Gwamnan Jihar Katsina, wato na Malam Aminu Bello Masari na jam’iyar A.P.C da Musa Nashuni na jam’íyyar P.D.P da Umar Abdu Tsauri Tata na jam’iyar APGA da kuma Sanata Yakubu Lado danmarke na jam’iyyar PDM. Dukkaninsu kowa ya nada zare, inda kuma kowanen su yake ganin shine zai sami nasara a zaben da za’a gudananr nan bada jimawa ba.Sai dai yan’iya magana na cwa idon ana babbakar Giwa ba’ajin kaurin Kusu.
Idon ana maganar ’yan’takar kujerar Gwamnan Jihar Katsina, dimbin jama’a sun fi maida hankalin ne ga manyan ’yan’takarar na manyan jam’iyu,wato Malam Aminu Bello Masari na Jam’’iyar adawa ta A.P.C da kuma Musa Nashuni na jam’iyar P.D.P, wanda ake kallon yana yin rawar sa ne da bazar Gwamna Ibrahim Shehu Shema,wanda ake ganin gwamnan ne ya tsayar da shi don ya gaje shi.
Tabbbas an ce hannu mai miya shi ne ake bi da lasa, idon muka dubi Musa Nashuni, wanda kowa yasan ba wai mutum ba ne fitacce a fagen siyasa ko aikin gwamnati ba. Domin dimbin jama’a basu taba ma sanin wai wani mutum shi Nashuni ba,a fagen siyasar Katsina ba, sai ga shi kwatsam gwamnan jahar katsina Shehu Shema ya jijjiboshi domin ya tsaya takarar kujerar gwamnan,da niyar ya gaje shi. Hakan ya zo ma Katsinawa da mamaki da kuma bazata. Idan muka dubi ma’aikatan gwamnati da duk wani mai bibiyar Shema, yana dan tashar nono ko’ince yana dan samun na fura daga Gwamna Shema.
To, a nan za mu iya cewa ba shi da wani dan takarar da ya wuce Musa Nashuni. Ba don komai ba, sai don gudun kada ya bijire wa mai gidansa, wanda kuma yin hakan zai iya sa ya rasa furar da yake samu daga mai gidan nasa.
Malam Aminu Bello Masari dan siyasa ne, wanda ya dade yana gumurzu a siyasar jihar mu da ma kasa baki daya,wanda kuma ya fito takarar kujerar gwamna ba sau daya ba ba sau biyu ba, Ya fito neman kujerar tun yana cikin jam’iyyar P.D.P, har lokacin da ya shiga cikin jam’iyyar adawa ta C.P.C da kuma A.P.C. Mutum ne wanda yasan harkokin siyasa, wanda hakan yasa ya fi Musa Nashuni sanin siyasa da harkokin siyasar baki daya,ta wannan gumurzu da Masari ya sha yi ne, ya sa yake da dimbin masoya, wanda wasun su suna tare da shi ne tun yana a P.D.P suke tare da shi, wasu kuma ya iske su ne a cikin jam’iyyar CPC, wadanda su ma suke tare da shi har zowa yanzu, sannan bugu da kari shigowar sa jam’iyyar A.P.C a nan ma ya tarar da dimbin jama’á, wanda suke tare da shi har yanzu. Manazarta lamuran siyasar Katsina suna yi wa Aminu Masarin kallon wanda zai iya kwasar dimbin jama’a a wannan siyasar.
Ganin yadda ya sha gwagwarmaya sosai, sannan Janar Muhammadu Buhari ya daga hannun shi a matsayin dan takarar sa, su ne dalilan da suka sa siyasar Katsina take daukar ido ga jama’ar jihar da ma kasa baki daya.Da fatan za mu yi zabe lafiya, mu gama lafiya, ita kuma hukumar zabe ta yi adalci, wajen gudanarwa da ba da sakamakon zaben a kan gaskiya da adalci, domin ci gaban jihar mu ta Katsina, da ma kasa baki daya.

Marubucin Haruna Muhammad Katsina, dan kungiya ne kuma shugaba a Muryar Talaka reshen Jihar Katsina. 070739205659.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu