siyasar Katsina ta koma masallatai
Ku ba ni dama domin inyi tsokaci a kan yadda siyasa ke gudana a massallatai a Jihar katsina, domin kuwa, jita-jitar cewa gwamnati mai ci a yanzu ta hana sauran jam’iyyun siyasa yin taro a filayen jama’a kamar su filin wasa da na folo da makamantansu. Lallai wannan kama karya bai kamata a ce ’yan […]
Ku ba ni dama domin inyi tsokaci a kan yadda siyasa ke gudana a massallatai a Jihar katsina, domin kuwa, jita-jitar cewa gwamnati mai ci a yanzu ta hana sauran jam’iyyun siyasa yin taro a filayen jama’a kamar su filin wasa da na folo da makamantansu. Lallai wannan kama karya bai kamata a ce ’yan sanda da jami’ai masu kaya sarki (unifom) da ma na gwamnati shiga cikin siya ba. Domin kuwa, wanda ake yi wa wulakanci Allah na iya ba shi mulki a lokacin da ya so. Wannan ya zama kalubale ga gwamnati da kungiyoyi masu rajin kawo gyara a shugabanci na gari a Jihar Katsina. Allah ya saukake. Amin.
A dubi abokan Aminiya
Edita ina so ka ba ni dama in kasance cikin abokan wannan jarida ta Aminiya, kuma shugabanni na kungiya makaranta na Jihar Kano, amma sai ga shi in mun aiko da sako ba a duba mu; ko laifi muka yi? Muna mika gaisuwarmu ga dukkan masoya wannan jarida tare da ma’aikatanta baki daya. Daga Garba madaki D/dawa.
Kwankwaso ne dan takara
Assalamu alaikum Aminiya ina son in shaida wa kasata Najeriya da cewa Kwankwaso shi ne gwarzon dan takara a jam iyyar APC, domin ci gaban kasa. Mutum mai aiki da adalci, mai neman cigaban kasa bai da bambancin addini. Mun ji, mun gani. Sai Rabi u Musa Kwankwaso, Shugaban kasar Najeriya. Daga Alasan Shu’aibu Badarawa, a karamar Hukumar Shinkafi, Jihar Zamfara,
A yi Hausar da kowa ya sani
Edita yana da kyau ku yi amfani da kalmomin da kowa ya sani wajen karatu. Misali kama amfani da (na) a wurare, maimakon sahihiyar Hausar da ake amfani da ita. Misali maimakon ka ce ina son in je, sai ka ce ina son na je. Ire-iren wannan da yawa cikin Aminiya, ya mayar da jaridar kamar don Kanawa kadai, wanda ba haka ba ne. Na biyu shi ne DODORIDO ; Ina sha’awar shafinsa, amma kash lauje-laujen da yake sawa yana yi min wuyar karantawa da ganewa. In Hausar Ghana ce yake amfani da ita, don Allah ya rage don mu fi ganewa.Nagode. Daga Yusuf Sani Sokoto 08109901031.
Ga manyan ’yan siyasa
Salam Edita Aminiya, ina son ka ba ni dama in yi tsokaci akan manyan ’yan siyasa na Arewa na jam’iyyar A.P.C, kamar Janar Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar da Rabi’u Musa Kwankwaso da su yi kokari su hada kansu, su zama tsintsiya madaurinki daya, wajen zama bisa teburin sulhu, domin sasantawa da junansu dangane da fitowa takarar shugaban kasa. Shawarata a gareku, ku fitar da mutum daya wanda ya cancanta ga karbuwa a wajen talakawa; wanda zai iya fitar da kangin da muke ciki yan zu. Da fatan Allah shi zabar mana shugabanni adilai, masu son ci gaban talakawa. Daga kasimu Aliyu Sardaunan Matasan Assada Jihar Sakkwato 08073785412.
Ga dan Majalisar Lere
Assalamu alaikum. Aminiya ina son ku mikamin sakona zuwa ga Ibrahim Lawal Nuhu Kayarda, dan Majalissar Lere, in dai zai tsayar da Umaru Yunusa takarar majalisa to wallahi zai samu matsala. Saboda hekara hudun da ya yi akan mulki bai yi wa talakawa aiki ba. Don haka talakawan Lere ba sa son tsoho, ya yi hakuri. Daga Matasan Kayarda
Ga Gwamnan Kano
Aminiya, ’yar amana don Allah ku gaya wa Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso, cewa mu talakawa ba ma goyon bayan takararsa ta shugaban kasa, ya je ya nemi takarar sanata, domin a 2015 APC ba wanda muka sani a takarar shugaban kasa sai Janar’ Muhammadu Buhari. Daga Musa’Unguwar Maiyasin, danja Jjihar Katsina. 08060611124,
Jan hankalin al’umma
Edita ina so a mika min sakon gaisuwata ga dukkan al’ummar kasa baki daya da jan hankali a kan siyasar kudi, wasu ma za ka ga sabulu za a ba su don su zabi dan siyasa. Don Allah mu gyara, mu zabi shugabannin da muka san za su yi mana aiki, ba son zuciya ba. Allah ya ba mu shugabanni nagari. Daga Uban Gwamna, Kwanar Jaba Maikatala resident.
Ga Jega na INEC
Salam. Edita don Allah ga sakona zuwa ga Jega to Jega zaman lafiyar kasar nan yana kanka, rashin zamanta lafiya, kuma yana kanka. Don haka in ka yi adalci kanka, inma ba ka yi ba kanka. Rayuwar da duk aka rasa wancan zabe laifin ka ne. Don haka yanzu in za ka gyara ga hanya. Hanyar ita ce tun daga shugaban kasa har kansila kowa ya sauka, a ba da rikon kwarya mu ga yadda za a yi magudi. Daga Sa’adu Abdullahi Wamakko, Jihar Sakkwato 08129296999/ 09030055445
Ga Gwamnan Kano
Salamun alaikum. Edita don Allah a mika min gaisuwata ga Gwamnan Kano, anyi taro lafiya Allah ya ba da nasara. Daga Muhammad Sani Limamin Makara kano.
Shawara ga Sakkwatawa
Assalamu alaikum. Don Allah Edita ka ba ni dama in ba mutanen Sakkwatto shawara, Jama’ar Jihar Sakkwatto mu dubi al’ummar Yobe da Maiduguri da Adamawa. dukkansu suna cikin tashin hakali, amma wani ya buda baki ya ce jam’iyya mai mulki ta ci gaba, ko shugaba ya zarce, ku tuna mutum ba ya kwanto wa kansa kura, domin duk abin da yaci wadanga jihohi ya ci mu.Don haka mu san maganar da muke yi.Allah ya gwada muna bayan masu cutar da al’ummar kasar nan da mabiyansa amin. Daga Nura Buhari Bodinga Lalas.07033155737
Ga Solomon Dalung
Salam Edita don girman Allah ka isar min da sako na ga Solomon Dalung aAllah ya ba shi Gwamna Jihar Filato, don gaskiya yana son zaman lafia. Daga Aliyu Kwatalaf, Sarkin Mangu street, Jos Jihar Filato. 08036565554
Jinjina ga matasan Yobe
Salam. Jinjina ta musamman ga matasan Yobe kun yi daidai, Allah yasa sauran matasan Najeriya su yi koyi da ku. Daga Umar Honestman, karamar Hukumar Numan Jihar Adamawa .
Ina dan majalisar Faskari?
Jama’a daukakin al’ummar karamar Hukumar Faskari suna cigiyar dan majalisars na jiha, Shehu Tsalha, ko hadarin kudi ya taso a majalisa ya tafi da shi. Daga Rufa’i Yakubu R/Godiya o8o65952353.
Godiya ga Edita
Edita nagode da shawarata da ka dauka, domin kuwa ’yan PDP Hausa ba su da wata kima a wurin mutane nagari. Allah ka shirya mu amin. Daga Masoyinku.
Akwai aiki a gaban APC
Edita don Allah kasanar wa manyan jam’iyyar APC cewa lallai akwai aiki a gabansu, saboda kawar da jam’iyyar PDP ba karamin aiki ba ne, musamman ture Jonathan akan kujera. To fa sai an yi da gaske. Mu kan sai dai mu ce Allah ya ba da sa’a. Daga Yahaya Ahmed Jabo Apapa Lagos 08026392800.
ga ’yan takarar APC
Zuwa ga Edita don Allah ka ba ni dan fili in yi kira ga ’yan takarar shugaban kasa na APC da cewa ba don al’ummar Arewa da talakawa suke yi ba, mugunta kawai suke yi wa Arewa. Idan ba haka ba su hada kansu su fito da mutum daya mana. Wannan abin da suke yi Arewa da ’ya’yanta kawai suke cuta. Ka dubi Kwankwaso wai shi ma ya fito don son zuciya da mugunta kawai don ya bata ruwa ba don ya sha ba. Allah ya saukake. Daga Bature Mai kilo kasuwar Sharada Kano.
Ga dan majalisar Sabon-gari
Salam don Allah Edita ka mika min sakon goyon baya na ga dan takarar majalisar tarayya ta Sabon Gari, Hon Yusuf Salihu Shaka. Daga Rabi’u 08036859012 .