Siyasar mangwaro tsakanin kasashen Indiya da Pakistan

Ga ala’ada a kasashen kudancin Asiya, duk shekara shugabannin Pakistan na aika wa takwarorinsu da ke Indiya kyautar mangwaro.Duk da shaharar siyasar mangwaron, dangantaka tsakanin kasashen da ke makwabtaka da juna ta yi tsami.Rahotanni sun nuna cewa, makonnin da suka gabata a lokacin bikin Sallar Idi, Firaministan Pakistan Nawaz Sharif ya aika wa Firaministan Indiya, […]

Siyasar mangwaro tsakanin kasashen Indiya da Pakistan
Siyasar mangwaro tsakanin kasashen Indiya da Pakistan

Ga ala’ada a kasashen kudancin Asiya, duk shekara shugabannin Pakistan na aika wa takwarorinsu da ke Indiya kyautar mangwaro.
Duk da shaharar siyasar mangwaron, dangantaka tsakanin kasashen da ke makwabtaka da juna ta yi tsami.
Rahotanni sun nuna cewa, makonnin da suka gabata a lokacin bikin Sallar Idi, Firaministan Pakistan Nawaz Sharif ya aika wa Firaministan Indiya, Narendra Modi kwalin Mangwaro.
Duk da haka babu jituwa a tsakanin su.
An aiko da goron sallar, duk da cewa ana ta faman yaki tsakanin Indiya da Pakistan a yankin Kashmir, inda aka kashe akalla muum biyar.
“An aiko wa Mista Modi mangwaro ta hannun jami’an Pakistan, duk da kasar ta zargi Indiya da kai farmaki a sararin samaniyarsu,” inji wani jami’in Indiya a jaridar The Hindustan ta kasar.
Mista Sharif ya aikowa Mista Modi kilo 10 na mangwaro, kilo 15 ga Shugaban kasar Indiya Pranab Mukherjee da kuma kilo goma-goma ga tsofaffin Firaminista Atal Behari bajpayee da Manmohan Singh.
Amma wannan siyasar mangwaro ba ta yi farin jini ba, saboda ba ta gyara dangantakar tsakanin kasashen ba.
A ranar Litinin ne Indiya ta dorawa Pakistan alhakin wani hari da aka kai a wata motar bas da kuma ofishin ‘yan sanda a garin Gurudaspur da ke arewacin jihar Punjab, inda mutane 10 tare da wani babban jami’in tsaro suka hallaka.
A farkon watan da ya gabata ma sojojin Pakistan sun ki amsar kyautar Sallah daga sojojin Indiya a dalilin rashin jituwar ta su.
Kyautar kayan zaki a tsakanin kasashen a lokacin bukukuwa ya zamo ala’ada, kamar kyautar mangwaro, amma ita Indiya ba ta mayar da tukwuici da mangwaro.
Indiya ta fi kowace kasa a duniya noman mangwaro, amma ba ta ba da shi a matsayin tukwuici ga makwabciyar ta Pakistan.
Pakistan ce ta biyar cikin kasashe a noman mangwaro kuma wasu kafofin sun bayyana cewa ba Indiya kadai ta ke turawa ba, ala’adar kasar ce ta aikawa shugabannin kasashe Mangwaro.
Indiya ce ta fi kowace kasa a duniya noman Magwaro, duk da cewar akwai musu tsakanin kasashen a kan ko ta wace kasa ce ta fi kyau.
“Zai yi kyau Indiya ita ma ta turawa shugabannin Pakistan Mangwaro,” inji wani dan siyasar Indiya, Mani Shankar Aiyar.
“Nayi aiki a ofishin jakadancin Indiya a birnin Karaci, kuma na san mangwaron Pakistan ta fi ta Indiya.”
Yawancin ‘yan kasar Indiya suna alfahari da mangwaron da ake noma wa a kasarsu, saboda haka baza su yarda da zancen Mista Aiyar ba.
Mista Modi ya karbi gayyatar da Mista. Sharif ya yi masa na ziyartar taron yankuna da za ayi a Islamabad a badi.  Ayesha Siddika, wata mai sharhi aka harkar diflomasiyya ta yi na’am da zancen Mista. Aiyar, inda ta ce, “Mangoro da wasan Kurket sune dabaru mafi dadewa da ake amfani dasu wurin daidadita siyasa a tsakanin Indiya da Pakistan, kasashen biyu basa maganar baka da juna.”
–An samo wannan rahoton ne daga BBC