Siyasar taro sisi

A kasar Haurobiya, an dade ana siyasar laluben taro sisi, wadansu kuwa har watanda suke yi da dukiyar al’umma.Don haka ko tantama babu, shi yasa Haurobiyawa ke fama da duhun dundumdurundum, a daidai lokacin da shagabanni ke cin duhu.Mu dai ga tashenmu nan kan wadanda ke fafutikar kwalemar taro sisi a lalitar kasar Haurobiya. Ga […]

Siyasar taro sisi

A kasar Haurobiya, an dade ana siyasar laluben taro sisi, wadansu kuwa har watanda suke yi da dukiyar al’umma.
Don haka ko tantama babu, shi yasa Haurobiyawa ke fama da duhun dundumdurundum, a daidai lokacin da shagabanni ke cin duhu.
Mu dai ga tashenmu nan kan wadanda ke fafutikar kwalemar taro sisi a lalitar kasar Haurobiya.

Ga wakar watanda:

Na ni guniya calka ko wahanda
Ginsamin nama watanda
Ga gasasshen kifi na banda
Fatar sa ta ganda
Romon kayan ciki ragadada
Toyayyar masa a tanda
A tuttulo ruwa daga randa
Malam ya handame kaza a kwano
A kawo kwaryar fura da nono
Masanin Sisi-da-sisi
Gwamnan assasa asarar asi
Asusunka babu ko asi
Samarin kusu sun yi watanda
E, GizBaba ya yi watanda
Ranar idi an yi watanda
Da kirsimeti an yi watanda
Dukiyar Haurobiya ta kare a watanda
Ana ta yi mana far-far da ganda
Ku binciko labarin Bagauda
Mai karfa-karfan karfin karkanda
Cilkowa tsuntsun watanda
Ku tashi mu tafi Uganda!

Na yi roko ga Ilahuna,
Wanda ya aiko Muhamadu Manzona
Hada da sahabbansa masoyana
Sanya in kadaiShi Mahaliccina
A daukacin mu’amala da ibaduna

Allahu Ka haskaka kirjina
Sanya a fasko manufar kalamaina
Yadda na jero a baitocina
In amfanar da mutanena
In zamto mai amfanin kaina

Na zizara Zinaru: zinariya
Amintattar jaridar Haurobiya
GizBaba mijin Bagizagiya
Da Dodon Dodanniya
Baban jinjinniya

Mun shigo batun tashe
A bara mun kwashi taushe
Mun yi nashe-nashe
A gidan Malam Bahaushe
Tuwo mai mai, nama da miyar taushe

GizBaba ya kake karatu,
Ko yin batu?
Da ka kan ga wa na-zomo kurtu
Ka yi ta surutu rututu
Tamkar Reuters mai bututun  batu:

“Tsuntsu
Sheka
Bishiya
Daji,”

Ga bakon Tagadas
Mai cimakar ca’ammas
Hutu sai mun je Bahamas
Malam ya zama mangas
Kun ji cas da as!

kurmus-kurmus
Kun ji motsin ca’ammas
A bakin mai kus-kus
GizBa ba na bulus
Ka tara matsabbai cunkus

Ka daina wasan  drama
Turawa ke drama
Larabawa sai tamsiliyya
Ga masalsala a Tunusiyya
Mu nemi dacen wata mai alfarma

Batun abinci
Ba ni da’yanci
Wai don na nuna kawaici
Sai aka  yi mini habaici
Har da barkwanci

Ana yi min barazana da  cici
Don a cusa mini takaici
Ga korafina cikin baitoci
Baffan Editoci
Kar ka ce na yi butulci

A watan rahama
Watan alfarma
A daina waftar gararuma
A yi fafutikar makoma
Wannan ita ce makama

Ni Dodo
Na farfajiyar Dodorido
Mai ’yan makaranta dodo-dodo
Mun ga masu laluben bado
Yana ruwa shimfide tamfar gado

Na juya siyasar kiyasi
A baitukan Imru’ul kaisi
Batun AbdelFatah al-Sisi
Da Shugaban Masar Muhammad Mursi
Dama-dama da kurda-kurda marar asasi

“Irhil! Irhil! Sisi
Mursi ra’isi.”

Misirawa na kyarar juyin sisi
’Yan uwan sun ga wallen al-Sisi
Saboda kauna ga Mursi
Zababben shugaba mai asasi
Haurobiyawa gareku masu darasi

Ba na bin bahasi
Ina masu neman taro sisi
Lado da Okonko da Lasisi
Ba ku da ko asi
An yi muku mursisi

Barden makamashi
Ya jefi al’umma da mashi
An jikkata a kowane sashi
Misirawa sun sha ruwan alburushi
Ana ta cilla musu harsashi

Amurka na bayan Sisi
Turai na bibiyar Sisi
Misirawa sun ja daga a bayan Mursi
An jefa musu waswasi
A dukufa yin Falaki da Nasi

kyale na-mujiya ya yi maka dubi
Su yi ta kawalniya a madubi
Suna ganin gazawa cike da aibi
Gajen hakuri na hana cimma rabi
Matsaloli na nan rabi da rabi

Mai taka-tsantsa na cimma burinsa
Mai gaggawa kan gaza kai ga nufinsa
Mai manufa ba ya nuna son ransa
Mu kiyayi shaidani da illarsa
Na yi ta’awuzi don kar in fada a tafarkinsa.

Sakon makaranta
Assalamu alaikum. ’Yan uwa dalibai Manzon Rabbu Makadaici (Tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya koyar da mu cewa idan aka tsinci kai kawunanmu a kwanukan sili da zagaye na karshen watan rahama, sai mu yawaita fadin: “Allahumma Innaka Afuwun Tuhibbul Afuwa fa Affu’al ni” Allah Ya Tsunduma mu Cikin Rahaniyyar Sa.
Daga Sabi’u Uba Yola 07032385544  07055417766 shugaban daliban Jihar Fullo-ke- damawa.