SLS: Ko an kashe biri ya yi barna
Babu wata magana da ‘yan Najeriya suka yi ta riritawa a ‘yan shekarun baya kamar kwabewar da Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi wa Sanusi Lamido Sanusi daga matsayin Gwamnan Babban Bankin Najeriya bagatatan, kuma hakan ya jawo kwarmato da gutsuri-tsoma yayin da jama’a da yawa suka yi ta furta albarkacin bakunansu. Ra’ayoyi game da […]
Babu wata magana da ‘yan Najeriya suka yi ta riritawa a ‘yan shekarun baya kamar kwabewar da Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi wa Sanusi Lamido Sanusi daga matsayin Gwamnan Babban Bankin Najeriya bagatatan, kuma hakan ya jawo kwarmato da gutsuri-tsoma yayin da jama’a da yawa suka yi ta furta albarkacin bakunansu. Ra’ayoyi game da wannan al’amari sun ta tuttudowa ba kakkautawa, kuma ko wannan ne da irin yanayinsa da yadda yake kamanta yadda bakin mai furtawa ya karkata, yana kuma bayyana irin miyau din da ya kwararo.
Sa’ilin da wasu ke ganin fafarar da Shugaba Jionathan ya yi wa danmajen Kano, Alhaji Sanusi Lamido Sanusi daga kujerar Gwamnan Babban Banki ta dace matuka don ya zamo tsuntsun da ya kira ruwan da ya jika shi sharkaf, wasu kuwa sun hakikance cewa wannan danyen aiki ne da ke tabbatar wa talakawan Najeriya cewa gwamnatin Jonathan tsumma ce makullin cuta wacce ke daure gindin azzaluman da ke sace dukiyar kasar nan wadanda suka yi katutu a ma’aikatu da hukumominta. Haka nan kuma jama’ar Najeriya sun kasa gane yadda reshe ya juye da mujiya, har aka kai ga dakatar mutumin da ya tona asirin ha’incin da ake tafkawa a ma’aikatar man fetur din kasar nan.
Irin wadannan mutanen da suka kasa gane kan-gadon Shugaba Jonathan game da wannan aika-aikar, cewa suke yi ai da ma sun san za a rina, domin kuwa da wuya wata gwamnati da aka kafa ba bisa gaskiya ba ta kyale wani ma’aikacinta ya yi mata hawan kawara, yana kuma yi mata tonon sililin da ke zubar mata da mutunci a idanun duniya. To wai shin akwai wata gwamnatin da macuta suka yi katutu a cikinta da za ta amince a karya mata tsinken tsire a ido, ko kuma a kabar da kwaryar kindirmon da ta tatso daga shanun sata, tana ta kurba? Ina! Kuma ai iyayen gidan masu tatike baitil-malin gwamnati karkaf ba za su yi lakamo, su kyale ya yi masu sakiyar da ba ruwa ba. Shi ya sa ala-kulli-halin sai an tozarta danmajen Kano.
Wannan shi ne kissar Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi, wanda bakinsa ya yanka masa wuya sakamakon zargin da ya yi na cuwa-cuwar wasu Dala miliyan dubu ashirin (kwatankwacin Naira miliyan dubu gida dubu da dari uku) a ma’aikatar man fetur ta kasa wanda aka ki bincikawa don wadanda ake zargi da yin sama da fadi da waccan dukiyar su ne shafaffu da mai a fuskar Shugaba Jonathan. Shi ya sa ake ta mamakin ganin yadda Shugaban ya ki yin adalci ga wannan al’amari, aka bi son zuciya kamar yadda aka saba a dukkan lokutan da aka tona asirin ‘yan lelen Shugaba Jonathan, kuma na hannun damansa wadanda suka fito daga karkara guda da shi.
Sa’ilin da takaicin dage Sanusi Lamido daga bisa mukaminsa bai kwaranye ba a zukatan talakawa, sai ga Shugaba Jonathan ya fito a tashar Talbijin ta kasa, yayin zantawa da ‘yan jaridu, yana cewa har yanzu dai Sanusi Lamido Sanusi ne Gwamnan Babban Banki, duk kuwa da cewa ya zabi wani da zai maye gurbinsa nan gaba, idan binciken da za a yi ya tabbatar da zargin almundahanar da ake yi masa.
To idan har an san da haka, kuma za a yi bincike game da rawar da ya taka a bakin aikinsa, me ya hana ba za a bi bahasin waccan maganar ta dala biliyan 20 da ya yi zargin sun bi shanun sarki ba a ma’aikatar mai ta kasa, a kuma dakatar da Minista Diezani Allison-Maduekwe tare da gagga-gaggan jami’an ma’aikatarta har sai an gama binciken batun inda wadancan kudin suka sargafe, don a kwantar da hankulan jama’a?
A takaice dai Shugaba Jonathan ya nuna cewa an yi gaggawa wajen daukar matakin dakatar da Sanusi tun kafin a tabbatar da gaskiyar zargin da wasu ‘yan yankin kudu-maso-gabas suka fi kururutawa, domin kuwa an dauki matakin da bai dace ba kamar yadda duniya gaba daya ke cewa. Daga cikin muryoyin da suka karkada kunnuwan jama’a game da nuna rashin dacewar haka akwai ta Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, mutumin da aka tabbatar da cewa ba safai yake shiga sharo ba shanu ba, domin kuwa kafin magana ta fito daga bakinsa yakan yi taka-tsantsan, ya auna, ya lailaya ta, ya yi kwana da kwanaki yana mata sabarta-juyarta a zuciyarsa don ya tabbatar da dacewarta a matsayin sahihiyar kalmar da za ta fito daga bakinsa, wacce ba za ta tayar da zaune tsaye ba.
Mai martaba Ado Bayero ya nuna cewa matakan da aka bi don kwabe Sanusi daga aikinsa ba su da ce ba, don rashin bin ka’idojin da aka gindaya kafin haka. Ashe ke nan ana iya cewa abin da ya karfafa wa San Kano gwiwa har ya kai shi ga furtawa bai wuce gaskiya tsagwaronta ba, domin abin da ya koro bera har ya fada wuta, ya fi wutar zafi. To ko Shugaban Jonathan zai fahimci gaskiya, ya kuma komo bisanta, ya kafa kwamitin binciken wadancan Dala miliyan dubu ashirin da aka ce sun salwanta? Idan ba haka ba kuwa to ana iya cewa Jonathan ya debo ruwan dafa kansa, Ko dai me za a yi da Sanusi ba a huce ba, domin ko an kashe biri dai ya yi barna.