SMEDAN ta horar da manoma dabarun kasuwanci
Hukumar Bunkasa kananan Masana’antu ta Najeriya [SMEDAN] ta shirya taron horar da manoman masara dabarun harkokin kasuwancin amfanin gona na masara, a karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna. Da yake jawabi a wajen bude taron horar da manoman manajan hukumar a ofishin hukumar da ke Kaduna, Badamasi Ya’u Barau ya bayyana cewa sun zabi […]
Hukumar Bunkasa kananan Masana’antu ta Najeriya [SMEDAN] ta shirya taron horar da manoman masara dabarun harkokin kasuwancin amfanin gona na masara, a karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna.
Da yake jawabi a wajen bude taron horar da manoman manajan hukumar a ofishin hukumar da ke Kaduna, Badamasi Ya’u Barau ya bayyana cewa sun zabi karamar Hukumar Lere ne wajen gudanar da wannan shiri, ganin cewa ita ce kan gaba a harkokin noman masara a kasar nan.
Ya ce jihohi 14 ne hukumarsu ta dauka don koya wa manoma dabarun harkokin kasuwanci a cikin kayayyakin amfanin gonar da suke nomawa don su dogara da kansu.
A cewarsa, gudanar da wannan shiri ba manoma kadai zai taimakawa ba, har ma’aikata za su iya rike wannan shiri a matsayin abin da za su dogara da kansu.
Ya ce a wannan shiri an debi mutum 50 a kowace jiha kuma an zabi kayayyakin amfanin gona daban-daban wajen gudanar da shirin.
“A Jihar Kaduna an dauki noman masara don haka muka dauki karamar Hukumar Lere a matsayin inda za mu koyawa manoman masara yadda ake harkokin kasuwanci a amfanin gona na masara’’.
Ya yi kira ga wadanda suka shiga wannan shiri su mayar da hankali kan abubuwan da aka koya masu domin su cigajiyar shirin.
A nasa jawabin jagoran wadanda suka amfana da wannan shirin a karamar hukumar Lere Malam Ya’u Aliyu Lere ya bayyana cewa mu dai mutanen karamar hukumar Lere mun gaji sana’ar noma ne.
Ya ce sanin kowa ne a Najeriya gabaki daya babu wata karamar hukuma da ta kai karamar hukumar Lere noman masara. ‘’Muna matukar farin ciki kan kawo wannan shiri.Kuma da yardar Allah za mu yi amfani da dukkan abubuwan da aka koya mana a wajen wannan taron bita’’. Shima a nasa jawabin wani shugaban manoma Alhaji Tasi’u Bako Na Bawa Saminaka ya bayyana cewa wannan shiri da gwamnatin tarayya ta kawo zai taimaki manoma wajen sarrafa kayayyakin amfanin gonar da suke nomawa.
Ya yi kira ga gwamnati ta cigaba da tallafawa manoman kasar nan ganin cewa yanzu hankulan al’ummar Najeriya ya koma kan harkokin noma.