So muke kotu ta ba da umarnin cire Kudu maso Gabas daga Najeriya —’Yan Arewa

Kungiyoyin Arewa sun ce hakan ne zai magance kashe-kashen da IPOB ke yi.

So muke kotu ta ba da umarnin cire Kudu maso Gabas daga Najeriya —’Yan Arewa

Nastura Ashir

Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya ta bukaci Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta umarci Majalisar Dokoki ta gaggauta cire yankin Kudu maso Gabas daga Najeriya, kafin kammala gyaran kundin tsarin mulki da take yi.

Kungiyoyin Arewan sun bukaci hakan ne a karar da suka shigar gaban kotun suna masu cewa cire yankin Kudu maso Gabas daga Najeriya zai magance rikice-rikice da asarar dukiya da ayyukan haramtacciyar kungiyar yankin ta IPOB ke haifarwa.

Masu shigar da karar — Nastura Ashir Shariff, Balarabe Rufa’i, Abdul-Aziz Sulaiman da Aminu Adam — sun ce cire yankin daga Najeriya shi ne mafi a’ala ga kasar, domin kar a mamaimata irin asarar rayuka da dukiyoyin biliyoyi da aka yi lokacin yakin basasar 1967 zuwa 1970.

Wadanda gamayyar kungiyoyin suke kara sun hada da Antoni Janar na Tarayya, Shugaban Majalisar Dattawa da Shugaban Majalisar Wakilai da Majalisar Dokoki.

Ya kamata a sa da mu —Lauyoyin Igbo

Tuni dai wasu lauyoyi daga yankin Kudu maso Gabas, karkashin jagorancin Chuks Muoma, Ukpai Ukairo, Ebere Uzoatu da Obi Emuka, suka bukaci kotun ta ba su damar kasancewa cikin jerin ake kara a matasyinsu na wakilan yankin Kudu maso Gabas.

A cewarsu, suna da abin da za su kare a karar, don haka suke neman a ba su damar shiga ciki, duk da cewa kungiyoyin Arewan da suka shigar da karar ba su ga dacewar su sanya mutanen yankin Kudu maso Gabas a cikin wadanda ake kara ba, domin kotun ta ji ta bakinsu.

A takardar da suka gabatar ta hannun Victor Onweremadu a ranar Litinin, ta ce bukatar da dattawan Arewa suka gabatar na neman a cire yankin Kudu maso Gabas daga Najeriya zai taimaka wajen kyautata rayuwar al’ummar kabilar Igbo da ke yankin.