‘So nake in kashe Donald Trump’
dan Birtaniyar nan, Michael Sandford, da ake zargi da kwace bindigar wani dan sanda a lokacin gangamin yakin neman zaben Donald Trump a birnin Les begas, ya ce ya so ya harbe Mista Trump din ne.A ranar Asabar ne dai matashin ya je kusa da dan sanda, inda ya shaida masa cewa yana son Trump […]

dan Birtaniyar nan, Michael Sandford, da ake zargi da kwace bindigar wani dan sanda a lokacin gangamin yakin neman zaben Donald Trump a birnin Les begas, ya ce ya so ya harbe Mista Trump din ne.
A ranar Asabar ne dai matashin ya je kusa da dan sanda, inda ya shaida masa cewa yana son Trump ya sanya masa hannu a wata takarda ne. Amma kafin ka ce kwabo, sai Michael ya yi wuf ya kai hannu ga bindigar dan sandan, kamar yadda BBC ta bayyana.
An gurfanar da shi gaban kotu ne ranar Litinin, kuma bisa bayanan kotu, Michael, mai shekara 19, ya ce ya yi takakkiya ne zuwa birnin Les begas, domin kawai ya kashe Trump.
Har ila yau, ya ce ya kwashe kusan shekara guda yana kitsa yadda zai kashe Mista Trump, yana cewa shi ma kuma ya san za a kashe shi.
Sai dai lokacin da kafar yada labarai ta Politico ta tambaye Trump, cewa ya yi, ta gidan talabijin ya samu labarin saboda babu wanda ya ba shi labarin al’amarin.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a iya fahimtar dalilan da suka sa matashin yin hakan ba.
A wani labarin kuma, a ranar Litinin ne Trump ya salami Manajan Yakin Neman Zabensa Corey Lewandowski.
Tafiyarsa na zuwa ne yayin da Trump ke fuskantar turjiya mai karfi daga manyan mambobin jam’iyyarsa saboda wasu kalamansa marasa dadi da kuma manufofinsa masu tsauri a kan ‘yan cirani da Musulmi.
Hakazalika, an caccaki Mista Trump saboda irin martanin da ya mayar bayan kisan mutane 49 a garin Orlando na kasar Amurka.