Soja 25 ’yan ta’adda suka kashe a Neja —Hedikwatar Tsaro

Jirgin yaƙin da ya faɗo a Jihar Neja ya yi hatsari ne a yayin da yake ɗauke da gawarwakin wasu sojojin da aka kashe

Soja 25 ’yan ta’adda suka kashe a Neja —Hedikwatar Tsaro

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa a taron ECOWAS a Abuja. (Hoto: KOLA SULAIMON / AFP)

Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta ce sojoji 25 ne suka rasu, ciki har da hafsoshi uku a harin da ’yan bindiga suka kai musu a Jihar Neja a farkon makon nan.

Alkaluman da rundunar ta fitar a safiyar Alhamis sun tabbatar cewa sojoji bakwai kuma suma samu rauni a musayar wutar da ya yi ajalin abokin aikinsu.

Kakakin rundunar, Manjo-Janar Edward Buba ya ce jirgin sojin da ya fado a Jihar Neja, ya yi hatsarin ne a hanyarsa ta zuwa kwaso sojojin da suka kwanta dama.

Ya ƙara da cewa gawarwakin sojoji 14 da aka kashe a baya suna cikin jirgin a lokacin da ya yi hatsarin.

Ya kashi takobin cewa duk wanda ya taba dakarun Najeriya zai yaba wa aya zaƙi.

“Duk ƙungiyar da ta kuskura ta taɓa mana dakarun, za ta ɗanɗana kuɗarta,”  in ji shi.

Ya yi bayanin ga ’yan jarida a Abuja ne ne bayan da farko rundunar tsaron ta tabbatar da harin, wanda ta ce sojoji sun kashe aƙalla ‘yan ta’adda 53.

Sojojin sun yi arangama da ’yan bindiga ne a yayin da suke hanyarsu ta kai dauki a wasu ƙauyuka da ’yan ta’adda suka kai hari a jihar ta Neja.

’Yan bindiga ƙarƙashin jagorancin Dogo Giɗe dai sun yi iƙirarin su ne suka harbo jirgin sojin.

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai