Soja 5 sun rasu a harin ’yan bindiga a Zamfara
Mahara sun bude wa sojoji wuta a iyakar jihohin Zamfara da Katsina.
Soja biyar sun kwanta dama a wani hari da ’yan bindiga suka kai musu a wani kauye da ke tsakanin jihohin Zamfara da Katsina.
’Yan bindiga sun bude wa sojojin wuta ne a kauyen Wanzamai da ke Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, a yayin da sojojin ke kokarin kai dauki a kauyen bayan sun ji karar harbe-harbe.
- An kama uba ya kai ’yan daba su doki malamin ’yarsa a makaranta
- Siyasar Kano: Taron Shekarau da wasu jiga-jigan APC ya tada kura
Wani ganau ya ce ’yan bindigar sun bude wa motar sojojin wuta ne a kusa da yankin ’Yankara da ke tsakanin jihohin Zamfara da Katsina.
Sashe Hausa na BBC ya ambato shi yana cewa, “Daga baya sai muka fahimci cewa mahara ne suka bude wa wata motar sojoji wuta kuma suka kashe duka sojoji biyar da ke ciki.”
“Ganin cewa babu sadarwa yankin muna sa ran sojojin na sintiri ne maharan suka far musu suka bude musu wuta suka kuma kwashe musu makamai.”
Mutumin ya ce shi da sauran matafiya da ’yan sanda ne suka kwashe gawarwakin sojojin da aka kashe.
Yanzu kimanin mako shida ke nan da gwamnati ta katse layukan sadarwa a sassan jihohin Zamafara da Katsina da zimmar dakile ’yan bindiga da kuma murkushe su.
Matakan tsaron sun hada da rufe wasu kasuwannin mako da haramta fataucin dabbobi da takaita sayar da man fetur da zirga-zirgar babura da sauransu.