Soja ruwa ya kashe wani ya sace motarsa a Abuja
Ni mai gadi ne kuma ma’aikacin jirgin ruwa a cikin sojojin ruwa. Bai yi mini kome ba; Na kashe shi ne don satar motarsa.”
Rundunar ’yan sanda a Abuja ta kama wani sojan ruwan Najeriya mai suna Abdul Rasheed Muhammad da laifin kashe Aminu, ɗan tsohon babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral I. I. Ibrahim (mai ritaya).
Kwamishinan ’yan sandan Abuja, Benneth Igweh, yayin da yake gabatar da wanda ake zargin a ranar Laraba, ya ce Muhammad ya kashe Aminu ne kuma ya sace motarsa makonni biyu da suka gabata.
A cewar Kwamishinan, an gano motar da wanda ake zargin ya sace.
“Kusan makonni biyu da suka gabata an yi wa Aminu Ibrahim, ɗan Vice Admiral I. I. Ibrahim (mai ritaya), tsohon babban hafsan sojin ruwa, fashi da makami, a unguwar Maitama da ke Abuja, sannan aka ɗauki motarsa ƙirar Prado SUV.
- Mun gano dalilin da ambaliya ta lalata gidaje 200 a Kaduna —SEMA
- Takarar 2027 ta fi karfin Atiku —Bode George
“Ina sanar da ku cewa, Abdul Rasheed Muhammad, wani jami’in sojan ruwa na Najeriya ne ya aikata kisan. Ya amsa laifinsa, kuma mun ƙwato motar Prado Jeep,” inji shi.
A zantawarsa da manema labarai, Muhammad ya ce shi ma’aikacin jirgin ruwa ne a cikin sojojin ruwa da aka tura gidan tsohon babban hafsan sojin ruwa.
Ya ce, “Ina aiki a gidan. Marigayin ya ce min yana so ya fita da daddare, wajen 11:30. Ya ce yana buƙatar tsaro.
“Don haka, na bi shi da bindiga ta. A hanya ya tsaya ya duba ATM ɗinsa, kamar zai sayi wani abu.
“Na yi tunanin wataƙila zan raka shi kasuwa ko wani wuri. Sai na fito ta ɗaya ƙofar, sai na harbe shi, na ɗauki motar na tafi.
“Ni mai gadi ne kuma ma’aikacin jirgin ruwa a cikin sojojin ruwa. Bai yi mini komai ba; Na kashe shi ne don satar motarsa.”