Soja ya caka wa dan acaba wuka a ciki

Wani soja ya shiga hannun ’yan sanda bayan da ya caka wa wani dan acaba wuja a wata mashaya a Jihar Legas.

Soja ya caka wa dan acaba wuka a ciki

Wani soja ya shiga hannun ’yan sanda bayan da ya caka wa wani dan acaba wuja a wata mashaya a Jihar Legas.

Kakakin ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da tsare sojan mai muƙamin Kofar bayan aukuwar lamarin a yanki Ikorodu.

Hundeyin ya ce, sojan da ake zargi, wanda ba a bayyana sunansa ba, “yana tsare kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.”

Wani dan sanda da ya bukaci a sakaya sunansa saboda ba a ba shi izinin yin magana da manema labarai ba, ya ce sojan da ke aiki a Bataliya ta 159nta Sojin Kasan Najeriya da ke Jigar Yobe, ya caka wa dan acaban mai suna Saheed Isa wuka ne sakamakon sabanin da suka samu.

Ya bayyana cewa sojan ya yi amfani da wata karamar wuka mai kama da bindiga ce ya soki dan acaban a cikinsa.

A bara, 2023, ’yan sanda a Jihar Ondo suka tsare wani soja mai suna Tope Kazeem bayan da ya caka wa wani farin hula hula.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta