Soja ya ceci barawon mota daga babbakewa
A safiyar Litinin da ta gabata ce wani barawon mota ya samu tsira da kyar bayan ya yi yunkurin sace wata mota a harabar Asibitin Reemee Medicare da ke GRA Bauchi. barawon ya sanya irin mabudin nan ne da ake kira ‘masta ki’ ya bude motar yana shirin tayar da ita sai mutane suka ankara […]

A safiyar Litinin da ta gabata ce wani barawon mota ya samu tsira da kyar bayan ya yi yunkurin sace wata mota a harabar Asibitin Reemee Medicare da ke GRA Bauchi. barawon ya sanya irin mabudin nan ne da ake kira ‘masta ki’ ya bude motar yana shirin tayar da ita sai mutane suka ankara suka rufe shi da duka suka watsa masa fetur za su sa sanya masa wuta, sai wani soja ya rungume shi. Ana cikin bugunsa tare da sojan ne sai motar wani hafsan soja ta zo wucewa, sojan ya tsayar da ita aka bude bayanta aka jefa barawon suka tafi ta yadda sojan ya ceci barawon ke nan. Bayan aukuwar lamarin ’yan sanda sun isa wurin amma sai suka koma da suka ji an tafi da barawon motar. Da ma barayi sun matsa wa wannan yanki mai kunshe da bankuna da ofisoshi musamman a harabar ginin Re-insurance House inda a kullum sai an dauke mota ko babur.