Soja ya harbe saurayi a cikin gidansu a Zariya

Duk da cewa samarin sun ruga sun shige gidansu, amma sojan ya harbi kofar gidan ya hallaka Isma’il

Soja ya harbe saurayi a cikin gidansu a Zariya

Wani saurayi dan shekara 18, mai suna Isma’il Muhammad, ya gamu da ajalinsa sakamakon harbin sa da ake zargin wani soja ya yi a yankin Samaru da ke Zariya.

Samaru gari ne da daruruwan ma’aikata da daliban Jami’ar Ahmadu Bello, kasancewar ita ma jami’ar a yankin take.

Ana zargin cewa an yi harbin ne da karfe 9 na safe a gidan su mamacin da ke layin Sarkin Pawa, a lokacin da sojojin suke gudanar da sintiri.

Shi dai Marigayi Isma’il Muhammad, kwanan na ya zana  jarabawar kammala sakandare a kuma yana da burin samun gurbin karatu a makarantar gaba da sakandare, kafin ya gamu da wannan kaddara.

Mahaifiyarsa, Zainab Sani, ta ce yana wasa ne tare da abokansa da ’yan uwansa a kofar gidan su, sai  suka hango motar sojoji ta doso inda suke kuma daya daga cikin sojojin ya nuna su da bindiga, shi ne suka ruga cikin gida suka rufe kofa.

Amma duk da haka sai sojan ya harbi kofar da shi marigayin ya dafe ta ciki domin hana sojojin shiga cikin gidan.

A don haka sai Zainab Sani ta bukaci a bi mata hakkin kisan da aka yi wa ɗan nata ta hanyar hukunta wanda ya aikata laifin.

Babban Kwamandan Runduna ta daya ta Sojojin Nijeriya, Manjo-Janar MLD Saraso ya kai ziyara gidansu mamacin domin jajanta musu.

Daga bisani ya gana da jama’ar yankin, inda ya ba su tabbacin cewa za a gudanar da cikakken bincike a kan batun, kuma rundunar na bukatar duk wanda yake da tabbacin gaskiyar yadda lamarin ya faru da ya bayyana domin a dauki kwakkwaran mataki.

Manjo-Janar Saraso ya ce abin da ya faru yana da ban takaici matuka, inda ya bukaci al’ummar yankin da su zauna lafiya kuma su kasance masu bin doka da oda.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS