Soja ya harbi matar aure a cikin gidanta
Ana zargin wani soja, wanda ba a bayyana sunansa ba, wanda yake aiki a shingen tsaron bakin Dogon Dala cikin Wusasa a gundumar Kufena da ke karamar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna da shiga gidan Malam Abdulsalami Abdullahi ya harbi matarsa mai suna Adama Shehu a kafada.Majiyarmu ta shaida wa wakilinmu cewa sojan ya bar […]
Ana zargin wani soja, wanda ba a bayyana sunansa ba, wanda yake aiki a shingen tsaron bakin Dogon Dala cikin Wusasa a gundumar Kufena da ke karamar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna da shiga gidan Malam Abdulsalami Abdullahi ya harbi matarsa mai suna Adama Shehu a kafada.
Majiyarmu ta shaida wa wakilinmu cewa sojan ya bar wajen aikinsa ne da ke kimanin mita sittin zuwa gidan, inda kafin ya shiga, ya tarar da wata mata tana diban ruwa a rijiya, ya yi barazanar zai harbe ta. Ita kuma ta nemi bahasi, amma dayake tana da goyo, sai ya ce mata ta ci albarkacin yaron da ke tare da ita.
kanen mijin Adama da aka harba, mai suna Adamu Shehu ya shaida wa wakilinmu cewa, “Tsakanin gidanmu da inda shingen sojoji yake da ’yan tazara, kuma shi wannan sojan yana yawan zuwa unguwarmu, ba mu san abin da ke kawo shi ba. Bayan ya iske mu misalin karfe biyar na yamma muna zaune dukkanmu, har da babban yayanmu, wasu yara biyu suna biye da shi a baya, kuma wadannan yaran ’yan cinkin Wusasa ne. Rijiyar da iyalanmu ke amfani da ita tana baya ne, kusa da gidanmu, sai ya sami matar kanena tare da yaranta uku, daya yana goye a bayanta, shi ne sai yake ce mata zai harbe ta. To kuma mu ba mu san abin da ya kai shi wajenta ba, har yake cewa zai harbe ta. Daga nan sai yaranta suka rugo suna fadin soja ya ce zai harbi mamanmu, ni kuma sai na fada ma wadanda muke tare, har da yayana, ‘Sojan nan fa kila yana da wata manufa, gara mu shige cikin gida’. Shiga gidanmu ke da wuya, ba a yi minti uku ba, sai muka ji harbin bindiga, sai na ji matan yayana tana salati, tana ihu, karnuka kuma suna ta haushi, yaran da take tare da su su ma suna ta kuka. Hankalinmu ya tashi, kamar ba zu mu fito ba. A hakan dai muka daure muka fito, sai muka ga wannan sojan yana janye da ita, ya rike hannunta ya nufi jikin motarsu. Muna isa wurin, sai muka ga jini na ta zuba, sai muka tambaye shi, ‘Ina za shi da ita?’ Sai ya ce zai kai ta asibiti ne. Muka ce ba mu yarda ba, a sauke mana ita, daga nan muka kai ta asibiti. Ka ji yadda aka yi”.
Yayin da Malama Adama take yi wa Aminiya bayani game da aukuwar lamarin, ta ce, ta dora tukunyar girki ke nan, sai ta ji cikinta ya dan juya, alamar tana bukatar zagawa, to a hanyarta ta zuwa zagayawar ce, sai kawai ta ji harbin bindiga a kafadarta.
Ta ce daga nan ne sai ta kama salati, tana kururuwa kan abin da ya same ta, sai shi wannan soja ya kwance damararsa ya kama hannunta ya daure, ya ja ta da nufin kai ta wajen motarsu. Dayake ba a san manufarsa ba, sai mutane suka nuna ba su yarda ba.
Kasancewar haka, sai aka kai ta wata asibiti da ke kusa da su, inda su kuma a asibitin suka ce abin ya fi karfinsu, “Sai dai nan asibitin Jami’ar Ahmadu Bello, inda aka kawo ni, kuma nake jiran aiki a wannan hannun nawa”. Inji ta.
Da wakilinmu ya waiwaiyi mijin Adama, Malam Abdulsalami Abdullahi, cewa ya yi al’amarin bai ji dadinsa ba, ta yadda aka keta shari’a, aka shigar masa gida tare da raunata masa mata.
Ya ce a halin yanzu dawainiya ta karu a kansa ke nan, domin ga ta yara guda shida, ga kuma uwarsu a asibiti.Babban yayansu Alhaji Baffa, ya kara bayanin cewa Allah ne Ya kwantar da al’amarin, domin abin na faruwa sai Anguwa tare Hakimi da kuma Kansilan unguwanmu tare da shugaban karamar hukuma, suka zo wurin suka jajanta mana, suka kwantar mana da hankali. Kansila da Hakimi tare da su aka je har asibiti, sannan shugaban ’yan sanda shi ma ya zo ya dauki butar da ke hannun Adama, lokacin da aka harbe ta, tare da kwasfar harshashin.
Game da zancen da ake yi na cewa sojan yana da yarinya ne a gidan, wadda ba ta son sa, Alhaji Baffa ya ce, “Wannan al’amari mu ma kanmu ba mu gane mashi ba, sai dai muna rokon Allah Ya takaita mana, Ya kuma kawo mana sauki, amma dai muna ganin rayuwa na zamani”.
Shi ko mijin Adama, Malam Abdulsalami, a game da batun yarinya, cewa ya yi “A’a, ni ba ni da wata babbar yarinya a gidan, in dai ba matata ya biyo ba”.
Wannan al’amari da ya auku ne ya sa matasa suka tunzura suka je shingen tsaron na sojojin suka rushe shi, amma dai wakilinmu ya lura cewa har zuwa lokacin da ya hada wannan rahoto, ba wani tashin hankalin da ya bayyana bayan aukuwar hakan.
Aminiya ta tuntubi sashen hulda da jama’a na sojoji da ke Zariya a inda Laftana Hashimu Abdullahi ya tabbatar da faruwar al’amarin, sannan ya bayyana cewa a halin da ake ciki sojan da ya yi aika-aikar yana tsare kuma an sanya kwamitin bincike don gano musabbabi da yanayin da lamarin ya auku.