Soja ya kashe dan sanda saboda tabar wiwi

Sojoji sun kashe dan sanda saboda kama wani soja da mota makare da tabar wiwi a Jihar Borno.

Soja ya kashe dan sanda saboda tabar wiwi

Sojoji sun harbe wani dan sanda har lahira bayan dan sandan da abokan aikinsa sun cafke wani soja wanda motarsa take cike da tabar wiwi.

Rikicin ya faru ne bayan sojan da ake zargin ya dauko kayan tabar wiwi a motarsa ya ki tsayawa  a  wani shingen bincike na ’yan sanda da suka tsayar da shi a garin Benishekh na Jihar Borno a safiyar Litinin.

Ganin sojan ya nemi tserewa ne ’yan sandan suka harbi tayar motar suka tilasta masa tsayawa suka bincike motar inda suka samu bayanta makil da tabar wiwi.

Wata majiar tsaro ta ce sojan da ke dauke da tabar wiwin da abokan aikinsa sun yi yunkurin hana ’yan sandan tafiya da motar, har abin ya kai ga harbin da aka kashe Sajan Ali, wanda yake yin ribas da motar, ya rasu nan take.

A halin yanzu wanda ake zargin yana tsare a sansanin sojoji, motar da aka kama da tabar wiwin kuma tana tsare a ofishin ’yan sanda na Benisheikh.

Wata majiyar tsaro ta ce sojan ya yi harbin ne da nufin hana a tafi da motar, “amma aka yi rashin sa’a ya samu dan sandan, yanzu haka sojan yana can a kulle ana bincikar sa.”

Wakilinmu ya kira kakakin ’yan sandan Jihar Borno, SP Kamilu Shatambaya, domin samun karin bayani, amma bai same shi ba.

A watan Fabrairun 2020 irin haka ta faru inda wani soja ya harbe wani dan sanda har lahira saboda wata hatsaniya a tsakaninsu a karamar hukumar Gwoza ta jihar.