Soja ya kashe direban kayan agaji kan na-goro a Borno

Sojan ya lakada wa direban motar kaan jinkan da yaronsa duka da kotar bindiga, a karshe direban ya ce ga garinku nan.

Soja ya kashe direban kayan agaji kan na-goro a Borno

Wani soja ya kashe direban motar kayan agaji da saboda kin ba shi na-goro a hanyar Dikwa zuwa Gamboru da ke Jihar Borno.

A safiyar Alhamis ce Sakataren Kungiyar Ma’aikatan Sufurin (NURTW) Ahmed Musa ya sanar cewa direban da sojan ya kashe ya dauke da kayan agaji ne zuwa N’djamena na Jamhuriyar Chadi.

Musa ya tabbatar cewa direban ya samu izini daga hedkwatar sojoji da kwamandan rundunar Operation Hadin Kai na Arewa maso Gabas, amma duk da “Sojan da ke wani shingen binciken ababen hawa ya nemi ya ba shi kudi.

“Amma ya bayyana wa sojan cewa kayayyakin jinkai ne a cikin motar kuma kwamandan rundunar ya sahale musu, inda  ya ba da takardar izinin.

“Duk da haka, sojan ya yi watsi da takardun ya lakada wa direban da yaronsa duka da kotar bindiga, har sai da direban ya suma, daga baya ya ce ga garinku nan.

“Haka muke rasa direbobi a sakamakon zaluncin da sojoji a hanyar Gambarou, shi ya sa muka yanke shawarar rufe hanyar har sai an dauki mataki,” inji shi.

Mukaddashin Daraktan Yada Labaran Rundunar Soji ta 7 da ke Maiduguri, Laftanar-Kanar Ajemusu Y Jingina ya tabbatar da labarin da kuma tsare sojan da samun ya kashe direban motar.

“Rundunar runduna ta 7 ta Najeriya ta samu koke daga kungiyar NURTW reshen Jihar Borno cewa wani soja ya kashe wani direban babbar mota mai suna Mohammed Bello a wani shingen bincike a kan hanyar Dikwa-Gamboru a ranar 26 ga watan Disamba, 2023.

“Samun korafin ke da wuya rundunarmu ta hanzarta daukar mataki, kuma kokarin ganin iyalan mamacin sun samu adalci, an kama sojan da ake zargi, kuma an fara bincike kan lamarin.”

Ya bayyana cewa rundunar da kungiyar NURTW sun kulla yarjejeniya domin ganin an shawo kan lamarin cikin lumana, da kuma tabbatar da adalci ga iyalan mamacin.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna