Soja ya naushe direba har lahira akan Naira 150
Darakta kuma jami’i mai magana da yawun rundunar soja ta 18 Laftanal Kanal Omale Ochuagwuba ya ce rundunar sojan ta kame sojan da ake zargi da kashe direban bas mai suna Bashiru Adebayo sakamakon jayayyar da ta shiga tsakaninsu kan kudin mota a tashar motar da ke unguwar Obalande a jihar Legas.Mista Joseph Agah wanda […]
Darakta kuma jami’i mai magana da yawun rundunar soja ta 18 Laftanal Kanal Omale Ochuagwuba ya ce rundunar sojan ta kame sojan da ake zargi da kashe direban bas mai suna Bashiru Adebayo sakamakon jayayyar da ta shiga tsakaninsu kan kudin mota a tashar motar da ke unguwar Obalande a jihar Legas.
Mista Joseph Agah wanda lamarin ya auku a kan idonsa a ranar Litinin din da ta gabata, ya ce, ‘’sojan ya rako matarsa tasha ne, ya sanya ta a motar da ke zuwa unguwar Yaba amma sai yaron motar ya nemi sai ta biya 150 kudin mota sannan kuma da naira 150 kudin kayanta. Nan take sojan ya nemi ragi amma yaron motar ya dage sai ta biya kudinta da na kayan da take dauke da shi, sai hakan ya janyo jayayya a tsakaninsu. Sai direban motar ya goyi bayan yaronsa, sai kawai fada ya kaure a tsaknin sojan da direban motar, nan take sojan ya kai masa naushi a wuya, sai kawai direban ya fadi kasa warwas, kafin a kai shi asibiti ya mutu. Sai sojan da matarsa suka yi kokarin gudu, amma sai direbobi da ke tashar suka afka musu da duka, ba don ’yan sanda sun cece su ba da an kashe su. Daga bisani sai sojan ya kira ’yan’uwansa sojoji da ke Barikin Dodon Baracks suka rika dukan jama’a ba ji ba gani’.
Laftanal Kanar Omale ya ba da tabbacin cewa ba za su bari lamarin ya tafi haka ba ba tare da daukar mataki ba.
Ya ce, ‘Sojan da ake zargi yana cikin farin kaya ne kuma ya raka matarsa tashar unguwar Obalende ne ta shiga mota zuwa kauyensu. Da suka isa tashar sai aka sanya kayanta a mota amma sai jayayya ta kunno kai a kan kudin mota. Sojan ya fada wa direban kudin motar ya yi yawa, sai kawai direban ya jeho kayan matar kasa ya ture sojan, sai suka fara fada. ’Yan’uwan direban sai suka shiga fadan suka rika dukan sojan. Sai matar sojan ta gudu Dodan barak ta ba da rahoton abin da ke faruwa, amma a lokacin da sojoji suka je wurin direban ya mutu’.
Abokin direban mai suna Taiwo Bolaje, ya bayyana direban da cewa mutum ne mai son zaman lafiya, wanda ya shafe shekaru fiye da 20 yana tukin mota a tashar.