Soja ya shafe mako guda da harsashi a cikin ƙwaƙwalwarsa
Wasu ma suna kira ga sojojin Rasha da su karrama shi da lambar yabo.

Kafofin yada labaran kasar Rasha sun yi ta jinjina wa wani sojan kasar a matsayin jarumi saboda ci gaba da fafatawa a yankin Kursk tsawon mako guda bayan harbin da aka yi masa a ka.
Mutumin da ba a bayyana sunansa ba, wanda aka ruwaito cewa yana cikin Brigade na 155 na Marine na Rukunin Pacific Fleet na Rasha, ya ci gaba fafatawa da sojojin Ukraine a Kursk lokacin da aka harbe shi.
- Nijar ta kori wasu kamfanonin China 3 daga ƙasar
- Faɗuwar farashin kayan abinci a watan azumi ta shammace mu – ‘Yan kasuwa
A lokacin an harbi hular kansa, amma yana tunanin tabbas harsashin ya huda cikinta.
Ya samu kumburi a saman idonsa, wanda daga ƙarshe ya sa idonsa ya fara rufewa, amma sai kawai ya ci gaba da harkokinsa, yana tunanin kumburin zai warke da kansa.
Sai dai bayan wani rauni da ya samu mai alaka da rauni ne ya sa sojan ya ziyarci asibiti, inda ya samu labarin cewa harsashin da ya soki kwakwarsa ya huda kokon kansa ya shiga kwakwalwarsa.
Hotunan sojan sun nuna ya samu mummunan rauni a wani wuri da harsashi ya ragargaza hularsa, inda gefan idonsa daya ya kumbura, amma ba a san yadda shi ko sauran sojojin suka gano raunin harsashin ba.
An yi zargin cewa mutumin ya ci gaba da fafatawa a fagen daga har tsawon mako guda ba tare da wata matsala ba, illa kumburin gefan idonsa.
Sai bayan da likitocin Rasha suka ɗauki hoton wurin sannan suka gano wani babban harsashin bindiga maƙale a ƙwaƙwalwar sojan.
Sun kalli lamarinsa a matsayin abin al’ajabi da ba kasafai yake faruwa ba, kuma a yanzu ana yaba wa mutumin saboda juriyarsa.
Wasu ma suna kira ga sojojin Rasha da su karrama shi da lambar yabo.
Wannan labari da ba a saba gani ba ya tuno da wani labari na yaƙi mai ban mamaki, inda sojan yaƙin basasar Amurka, Jacob Miller, wanda ya rayu tsawon shekara 50 bayan an harbe shi a goshi inda aka yi masa aiki a kwakwalwarsa.
Hotunansa da wani rami da ake gani a goshinsa na ta yaɗuwa a shafukan sada zumunta a yau.