Soja ya yi wa mahaifiyarsa kisan gilla a Kaduna
Ya yi mata dukan Kawo wuka sannan ya yi ta caccaka mata wuka har ta mutu
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kaduna ta kama wani soja mai shekara 30 da ake zargi da yi wa mahaifiyarsa kisan gilla ta hanyar sossoka mata wuka.
Majiyarmu ta ce lamarin ya faru ne a ranar Talata 29 ga watan Disamba, 2020.
Majiyar ta ce sojan mai suna Damilola Thompson Charles ya koma gidan mahaifiyarsa a Kaduna ne bayan ya samu rauni daga wani harin Boko Haram da ya rutsa da shi a Jihar Barno.
“Da fari ya yi wa mahaifiyar tashi dukan kawo wuka har ta kasa tashi, lamarin da ya sanya makwabta suka ankarar da ‘yan sanda, kafin daga bisani suka sako shi, inda makwabta suka bai wa mahaifiyar tasa hakuri ta kyale shi ya ci gaba da zama a gidan.
“Ya far wa mahaifiyar tasa mai suna Modukpe Thompson ne lokacin da tashirya za ta fita coci, inda dan nata ya yi ta caka mata wuka, har sai da daya daga cikin wukaken da ya yi amfani da ita ta karye a jikinta” a cewar majiyar.