Sojan da ake zargi da kashe Bafulatana bayan yi mata fyade ya kai karar ’yan sanda
Sojan nan da ake zargi da yi wa wata Bafulatana matar aure fyade tare da kashe ta, a yankin Deidei da ke Birnin Tarayya, Abuja, ya kai rundunar ’yan sandan Abuja kotu, inda yake neman diyyar Naira miliyan 20 kan tsare shi da aka yi a sashin binciken manyan laifuffuka (CID) na rundunar a lokacin […]
Sojan nan da ake zargi da yi wa wata Bafulatana matar aure fyade tare da kashe ta, a yankin Deidei da ke Birnin Tarayya, Abuja, ya kai rundunar ’yan sandan Abuja kotu, inda yake neman diyyar Naira miliyan 20 kan tsare shi da aka yi a sashin binciken manyan laifuffuka (CID) na rundunar a lokacin gudanar dan bincike, kamar yadda wata majiyar rundunar ta shaida wa Aminiya. Lamarin dai ya faru ne a ranar 27 ga Masris din bana a kusa da wata rugar Fulani da ke kusa da Deidei Janshan, inda matar ke sayar da nono wanda kuma bai nesa da shingen bincike na soja da wanda ake zargin ke aikin tsaro. A lokacin da lamarin ya faru jama’ar da suka garzaya wajen bayan sun ji ihun matar sun yi ta bugun sojan kafin wasu sojoji su cece shi tare da tserewa da shi. Bayan yi masa jinya, sashin binciken manyan laifuffuka na ’yan sandan ya gudanar da bincike a kansa, sai dai a daidai lokacin da ake shirin shigar da maganar kotu sai wata tawaga ta soji ta karbi al’amarin don gudanar da nata bincike, tare da alkawarin sake mika shi ga ’yan sanda. Bayanin da Aminiya ta samu ya tabbatar da cewa, maimakon dawo da wanda ake zargin don fuskantar shari’a, sai ga wanda ake zargin ya shigar da ’yan sanda kara. Sai dai majiyar ’yan sandan ta ce bangarenta ya shigar da kara a daya daga cikin manyan kotunan Abuja, bisa zargin sojan da aikata fyade da kisan kai.