Sojan gonar rediyon Muryar Amurka ya shiga hannu a Benin
An kama mutumin da ake zargi cewa ya dade yana yi wa Sashin Hausa na muryar Amirka (b.O.A) Sojan gona a garin Benin jihar Edo, wanda ake zargi kuma shi ne Faruk Yakubu mai kimani shekaru 40 da haifuwa, kuma dan asalin karamar hukumar Kiyana ta Jihar Nasarawa ne. Dubunsa ta cika ne a lokacin […]
An kama mutumin da ake zargi cewa ya dade yana yi wa Sashin Hausa na muryar Amirka (b.O.A) Sojan gona a garin Benin jihar Edo, wanda ake zargi kuma shi ne Faruk Yakubu mai kimani shekaru 40 da haifuwa, kuma dan asalin karamar hukumar Kiyana ta Jihar Nasarawa ne. Dubunsa ta cika ne a lokacin da ya ce shi ne wakilin muryar Amurka na Neja-Delta mai aiki da sashin Hausa na muryar Amurka, ya kuma yi hira da Shugaban al’ummar Arewa mazauna Jihar Edo, Alhaji Badamasi Saleh, amma bayan kammala hirar sai ya nemi ya ba shi wasu kudi, a nan ne asirinsa ya tonu.
Daga nan a take Alhaji Badamasi ya dauki waya ya kira daya daga cikin ma’aikatan b.O.A din na gaskiya da suke Abuja inda ya shaida masa yadda wannan mutumin ya zo masa har suka yi hira da shi, don haka nan take sai wakilin b.O.A din na gaskiya ya ce a rike shi, a kai shi ga hukumar ’yan sanda domin Wakilin b.O.A Umar Faruk Musa ba ya aiki a Neja Delta. Don haka ba tare da wani bata lokaci ba Alhaji Badamasi ya kira ’yan sanda suka zo, suka kama Faruk Yakubu zuwa ofishinsu na shiyyar Oba market da ke Ring Road, inda aka aka tsare shi.
‘’A yadda muka yi har muka kama shi Faruk Yakubu, shi ne, muna zaune wurin karbar gaisuwar ta’aziyya, sai wannan Faruk Yakubu ya zo ya same mu, ya ce yana neman shugabannin ‘yan Arewa mazauna Jihar Edo, sai aka ce da shi gani nan; sai ya ce da ni in zo ai shi wakilin Muryar Amurka ne, wato rediyon bOA na Neja-Delta. Sai na tambaye shi sunansa, ya ce sunansa Umar Faruk Musa sai ya nemi mu yi hira akan abin da ya shafi zabe. Da muka gama wannan hira sai ya bukaci in kai shi Ofishin PDP. Kuma bai hakura ba, sai ya nemi in ba shi kudi sai na cire Naira 5000 na ba shi, daga nan na fara tunanin shi ba dan jarida na gaskiya ba ne. Ya ce in kai shi wurin shiga mota zuwa Bayelsa, wai Abubakar Lamido yana can yana jira ya kai masa rahoto zai aika zuwa bOA. Sai na ce mu je kaci abinci kafin ka tafi.
Na gaya masa wannan domin in samu lokaci in kira ma’aikatan bOA na Abuja kuma na buga na gaya musu, inda suka ce karya yake yi. Sai na mika masa waya domin ya yi magana da su, daga wannan na fahimci cewa ba shi da gaskiya, sai na ce da shi mu tafi in kaika wurin shiga mota, sai ya bini na kai shi wurin ‘yan sanda na shiyyar Oba Market, na ce masa a nan ne bOA na gaske suka ce in kawoka,” inji shi.
Faruk Yakubu wani mai matsakaicin tsayi ne, kuma yana dingishi kadan, fari da shi irin na masu amfani da irin man nan mai maida baki ya zama fari, kuma yana da dan fadin fuska da manyan idanu, amma ba sosai ba, tare da alamar sanko kadan agaban goshisa zuwa tsakiyar kansa; yana da hana karya, amma ba shi da gemu. Yana sanye da riga safari da wandonta mai launin madara, tare da takalma sawu ciki idan kuma yana Magana sai ya taushe harshe kuma yana da wushiriya a hakoransa na sama.
Da mai laifin ya shig ahannun ’yan sanda, sai ya tabbatare da laifinsa.
‘’Wannan kuskure ne don Allah na roki arziki ku taimaka ku yafe mini ba zan sake ba,” a cewarsa, inda kuma a cikin bayaninsa ya kwatanta da cewa wannan ba shi ne karonsa na farko da yake aikata hakan ba.
‘’Na taba yin irin wannan a Byelsa, amma ba wanda ya gane kuma na taba aiki da gidan radio na Jigawa a tsakanin shekarun 1995-1996 sai na barsu na koma na kama aikin koyarwa a makaranta. Don Allah ina rokon shugaban bOA ya yi mini afuwa ,ina da matan aure biyu da ‘ya’yana uku na barsu a garin lafiya Jihar Nasarawa,’’ inji shi.
Babban jami’in ‘yan sanda na shiyyar Oba Market da ke tsakiyar garin Benin D.P.O Mista Aigbeo Aghahowa ya tabbatar da faruwar hakan, kuma ya ce Shugaban al’ummar Hausawa Alhaji Badamasi ya kawo mana wani da ake zargin yana yi wa gidan Radio shashin Hausa na Amurka sojan gona. Don haka a yanzu muna tsare da shi, har sai mun kare irin namu binciken na ‘yansanda kafin mu mika shi kotu, a cewarsa.