Sojan Najeriya sun rutsa ’yan Boko Haram a Pulka

Dakarun Najeriya da suka darkaki dajin Sambisa, sun rutsa da ’yan Boko Haram a yayin da suke tserewa a kauyen Pulka kusa da garin Gwoza, inda suka yi musu kaca-kaca a daren Lahadin da ta gabata, kamar yadda majiyar sojojin ta bayyana.Kanar Sani Usman Kuka-Sheka, Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Sojin Najeriya ya bayyana […]

Sojan Najeriya sun rutsa ’yan Boko Haram a Pulka
Sojan Najeriya sun rutsa ’yan Boko Haram a Pulka

Dakarun Najeriya da suka darkaki dajin Sambisa, sun rutsa da ’yan Boko Haram a yayin da suke tserewa a kauyen Pulka kusa da garin Gwoza, inda suka yi musu kaca-kaca a daren Lahadin da ta gabata, kamar yadda majiyar sojojin ta bayyana.
Kanar Sani Usman Kuka-Sheka, Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Sojin Najeriya ya bayyana cewa, a yayin wannan arangama, da dama daga cikin ’yan Boko Haram din sun rasa rayukansu, a yayin da suka yi nasarar kama guda daya da ransa. Dakarun kuma sun yi nasarar kwato miyagunn makamai da suka hada da manyan bindigogi da alburusai masu girman milimita 7.62 da asusun alburusan bindiga guda 47 da gurneti na hannu guda 36 da kuma kwafsan alburusai da dama.
A wata arangamar makamanciyar wannan, dakarun na soja sun kara darkake wasu karin ’yan ta’addar a Buni Yadi. Sun kuma yi nasarar kwato mota kirar Toyota Hilud da akwatuna biyu makare da alburusai masu girman milimita 7.62 da kuma wasu abubuwan fashewa.