Sojar da ta ci zalin mai yi wa kasa hidima ta shiga hannu
Za a hukunta hafsar sojar da ta rika kwara wa mai yi wa kasa hidima ruwan kazanta.
Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta yi ram da wata hafsar sojinta da ta ci zarafin wata mai yi wa kasa hidima, ta hanyar kwara mata ruwan kazanta a bainar jama’a.
Rundunar ta lashi takobin hukunta hafsar sojin, wadda bidiyon yadda ta ci zarafin mai yi wa kasar hidima a baina jama’a a Kalaba, Jihar Kuros Riba ya karade shafukan sada zumunta.
- Masu zagin Buhari a fili na zuwa Aso Rock su debi girki —Adesina
- Takaddama Kan Yi Wa Malaman Jihar Kano Gwajin Kwakwalwa
Bidiyon wulakancin da sojar ta yi wa mai yi wa kasar hidima ya tayar da kura, inda masau sharhi a kafafen sada zumunta ke ta kira a hukunta sojar, suna kuma bayyana yadda su ma sojoji suka wulakanta su ko suka ci zalinsu.
Bayan bidiyon da dan jarida Agba Jalingo ya fara yadawa ya tayar da kura ne Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya Onyema Nwachukwu, ya ce an gano sojar da ta yi aika-aikar, har ta nemi afuwar mai yi wa kasar hidima da kuma iyalanta.
Birgediya Nwachukwu ya nemi afuwar al’ummar Najeriya game da wuce gona da irin sojar, wadda ya tabbatar cewa za ta fuskanci hukunci.
“Mun lura da wani bidiyo a kafafen sada zumunta, wanda a ciki wata hafsar soji take wulakanta wata mai yi wa kasa hidima a Kalaba, Jihar Kuros Riba.
“Rundunar Sojin Najeriya ta yi tir da abin da hafsar ta yi wanda ya zubar a mutuncin rundunar. Wannan rashin daraja da ta yi ko kusa bai yi kama da matsayin rundunar ba kuma ba za ta lamunce shi ba.
“An gano lamarin ya faru ne a Birget na 13 da ke Kalaba kuma nan take Kwamandan ya kafa kwamitin bincike wanda ya gano hafsar sojin sy kuma hukunta ta na wucin gani kafin a furganar da ita ita a gaban kotun soji.
“Amma zargin da ake yi cewa hukumomin soji na kokarin yin rufa-rufa ba gaskiya ba ne, Rundunar Sojin Najeriya na da kwarewa kuma ba za ta lamunci duk wani nau’i na rashin ladabi ba.
“Muna tabbatar wa jama’a cewa ba za mu lamunci irin wannan wuc gona da iri ba daga jami’anmu.
“Rundunar sojin Najeriay tana tabbatar wa ’yan Najeriya cewa suna da cikakken ’yancinsu na dan Adam, kuma duk sojan da ya keta hakkin zai yaba wa aya zaki.
“Saboda haka mun rokon al’umma da su ci gaba ad kawo rahoton irin wadannan saba doka domin muna da teburin kare hakkin bil Adama a duk sansanoninmu domin hukunta sojoji masu kunnen kashi.
“Rundunar Sojin Najeriya na neman afuwa daga mai yi wa kasar hidima da iyalanta da Hukumar Kula da Masu YI wa Kasa Hidima da daukacin Najeriya game da cin zarafin da aka yi wa mai yi wa kasar hidima.”