Sojin sama sun kashe ’yan bindiga 30 a Katsina da Borno — NAF
An gudanar da samamen ne a kusa da Bakai, da Bakarya da kuma maɓoyar ‘yan bindigar ‘Yartsintsiya
Rundunar Sojin Saman Najeriya NAF ta ce rundunoninta na Operation Hadarin Daji da Haɗin Kai sun fatattaki ’yan bindiga 30 a samamen da suka kai musu da jiragen sama a maɓoyarsu da ke jihohin Katsina da Borno.
Daraktan hulɗa da jama’a da yaɗa labarai na rundunar sojin, AVM Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.
- Muhimman dokoki 10 a shekaru 25 na Dimokuraɗiyyar Najeriya
- An Dauki Sabbin Malamai Guda 5,000 A Jigawa
Gabkwet ya ce, samamen da rundunar sojin sama ta Operation Hadarin Daji ta kai a yankin Arewa maso Yamma a ranar 27 ga watan Mayu, ya yi nasarar kawar da wasu ‘yan bindiga da ke biyayya ga wani ƙasurgumin ɗan ta da ƙayar baya da aka fi sani da Babura.
Ya ce, an gudanar da samamen ne a kusa da Bakai, da wasu a Bakarya da kuma maɓoyar ‘yan bindigar ‘Yartsintsiya a Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara ta Katsina.
A cewarsa, sahihan bayanan da aka samu bayan samamen saman da aka kai sun nuna cewa an kashe ‘yan tada ƙayar bayan kusan 30.
Ya ce, an kuma tabbatar da cewa Babura da ƙyar ya tsira daga halaka, yayin da aka kashe akasarin ‘yan tawagarsa.
Gabkwet ya ce, rundunar Operation Hadin Kai ta kuma kai makamancin wannan samamen ranar Litinin a a wata maɓoyar ‘yan bindigar da ke yankin Tumbun Fulani a gabar Tafkin Chadi.
Ya ce, an ba da izinin kai samamen ne bayan da hukumar leƙen asiri ta gano dabarar da ‘yan ta da ƙayar bayan ke yi na komawa sabbin maɓoya da kuma tafiyar da kayan aikinsu.
“Idan an tuna cewa wannan wuri ne jirgin saman NAF ya kai hari a ranar 26 ga Satumba da 28 ga Satumbar 2023, tare da kawar da ’yan ta da ƙayar baya da yawa tare da lalata makamansu.”