Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Ana kyautata zaton waɗanda aka kashe ‘yan sa-kai ne.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Sojojin Saman Najeriya, sun yi kuskuren kashe mutum 16 a yankin Zurmi da ke Maradun a Jihar Zamfara, yayin da suke kai wa ’yan bindiga farmaki.

Rahotanni sun nuna cewa mafi yawan waɗanda aka kashe ’yan sa-kai ne da ke yaƙi da ’yan bindiga.

Bayanai sun ce ’yan sa-kai sun nemi taimakon sojojin sama wajen murƙushe ’yan bindigar da suke faɗa da su.

Amma sojojin sun yi kuskuren ɗaukar su a matsayin ’yan bindiga, tare da kai musu hari.

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya aike da saƙon jajensa ga iyalai da ’yan uwan waɗanda suka mutu.

A gefe guda yaba wa ƙoƙarin sojojin wajen yaƙi da ’yan bindiga a jihar.

Sanarwar gwamnatin jihar ta miƙa ta’aziyya ga ’yan sa-kai na Tungar Kara a Ƙaramar Hukumar Zurmi, waɗanda suka jajirce wajen kare al’umma daga barazanar ’yan bindiga.

Rahotanni sun ce ’yan sa-kai na kan hanyarsu ta barin Gidan Makera a yankin Boko lokacin da harin ya faru, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar 16 daga cikinsu.

Wannan lamari na zuwa ne makonni bayan da wasu ’yan sa-kai sama da 30 suka rasa ransu a Jihar Katsina sakamakon harin ’yan bindiga.

Masana sun danganta irin waɗannan kuskuren ga rashin isasshen musayar bayanai tsakanin ’yan sa-kai da jami’an tsaro, wanda ke haifar da mummunan sakamako a kan fararen hula.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7