Sojoji 2 sun rasu bayan motarsu ta taka bam a Sakkwato
Yanzu haka ‘yan bindiga sun fara sauya salon kai hare-hare a Sakkwato.
Sojoji biyu sun rasu, yayin da wani ɗaya ya ji rauni bayan motarsu ta taka bam da ake zargin ’yan bindiga sun dasa a hanyar Tiɗibale da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato.
Mai kula da harkokin tsaro a yankin Gabashin Sakkwato, Bashir Altine Guyawa Isa ne, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.
- Jigawa na samar da kashi 40 na alkamar da ake nomawa a Najeriya – Shettima
- An horar da manoman tumatir 100 kan dabarun rage tasirin sauyin yanayi
A cewarsa, lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 1 ga watan Yuli, 2026.
“A yau Laraba, ’yan ta’adda sun sake dasa bam a hanyar Tiɗibale da ke Ƙaramar Hukumar Isa.
“Motar sojoji ta taka bam ɗin, inda sojoji biyu suka rasa rayukansu, yayin da wani ya samu raunuka kuma yana karɓar magani a asibiti,” in ji shi.
Ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Sakkwato da ta ƙara ƙaimi wajen magance matsalar tsaro a yankin Gabashin jihar.
“Wannan sabon salon da ’yan bindiga suka ɗauka na amfani da bam ya ƙara tayar da hankalin al’ummar Gabashin Sakkwato, musamman mazauna Ƙananan Hukumomin Isa da Sabon Birni,” in ji shi.
Ƙoƙarin jin ta bakin Rundunar Sojin kan lamarin bai yi nasara ba.
Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindigar sun canza salo, inda suke kai hare-hare ƙauyuka lokacin damina, musamman idan ruwan sama ya fara sauka.
Haka kuma, sun fi amfani da dasa bama-bamai domin kai hari ga jami’an tsaro maimakon fafatawa da su kai-tsaye.