Sojoji 2 sun rasu yayin da motarsu ta taka bam a Sakkwato 

Kawo yanzu babu wata sanarwa a hukumance kan adadin waɗanda suka rasu a yayin harin.

Sojoji 2 sun rasu yayin da motarsu ta taka bam a Sakkwato 

Aƙalla dakarun soji biyu ne suka rasu, yayin da wasu da dama suka jikkata, bayan da motarsu ta taka wani bam da aka dasa a garin Bargaja, Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato.

Rahotanni sun nuna cewa sojojin suna kan hanyar zuwa kai wa mazauna garin ɗauki ne bayan ’yan bindiga sun kai musu hari da sanyin safiyar Asabar, tsakanin ƙarfe 12:30 zuwa 3 na dare.

Mazauna yankin sun ce ’yan bindiga sun mamaye garin Bargaja, inda suka dinga harbi kan mai uwa da wabi, lamarin da ya tilasta wa jama’a neman taimakon sojoji.

Amma kafin isowar su, an ce an dasa bam a hanyar Isa zuwa Bargaja.

Wani mazaunin yankin ya ce motar sojojin na kan hanyar zuwa ceton jama’a lokacin da ta taka bam ɗin.

Ya ƙara da cewa wani soja da ya ji rauni ya shiga zuwa cikin gari yana neman taimako.

Wasu mazauna garin sun ce sun ga gawarwakin sojoji biyu, yayin da wasu suka ce adadin zai iya fin haka.

An ce daga baya an kwashe gawarwakin zuwa Sakkwato.

Hukumomi ba su tabbatar da ainihin adadin waɗanda suka mutu ba.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu jin ta bakin ’yan sanda, sojoji ko Ƙananan Hukumomi ba.