Sojoji a Bayelsa sun gabatar da ’yan tada zaune

Sojjoin Birged na biyu na sojin Najeriya da ke Yenagoa a Jihar Bayelsa, sun gabatar wa manema labarai wasu mutum 17 da ake zargi sun tada zaune-tsaye a jihar lokacin da aka yi zaben Gwamna a kwanakin baya.Da yake gabatar da wadanda ake zargin, Kwamandan Birged din, Birgediya Janar Stebenson Olabanji ya ce ya yanke […]

Sojoji a Bayelsa sun gabatar da ’yan tada zaune
Sojoji a Bayelsa sun gabatar da ’yan tada zaune

Sojjoin Birged na biyu na sojin Najeriya da ke Yenagoa a Jihar Bayelsa, sun gabatar wa manema labarai wasu mutum 17 da ake zargi sun tada zaune-tsaye a jihar lokacin da aka yi zaben Gwamna a kwanakin baya.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin, Kwamandan Birged din, Birgediya Janar Stebenson Olabanji ya ce ya yanke shawarar nuna wa manema labarai wadanda ake zargin ne don kada su shafa wa sojoji kashin kaji, domin a lokacin zaben jami’ansa sun yi aikinsu cikin natsuwa da kwanciyar hankali; shi ya sa ma suka samu katarin kama su.
Matasan, inji kwamandan, an kama wasu daga cikinsu a yankin Ekeremor, sai wasu uku dauke da katin zabe da kuma kayan da aka same su da su, wadanda yawancinsu matasa ne sun hada da bindigogi, adduna da sauran miyagun makamai. Tuni rundunar ta mika su ga ’yan sanda.
A waje daya kuma, rundunar ’yan sandan Jihar Bayelsa ta kara da cewa tun a jajibirin zaben jihar ne rahotannin shigar da miyagun makamai a karamar Hukumar Ijaw ta kudu ya rika zuwa musu, musamman yankin Olabinji da aka rika jin karar harbe-harbe da kuma kauyukan Oporoma, hedkwatar karamar Hukumar Ijaw ta kudu.
Daga karshe, rundunar ta ’yan sandan ta bayyana kara cafke wasu da bindigogi da sauran makamai kuma da zarar sun gama bincike kotu za su mika su.