Sojoji ba su da abin yi a kafafen sada zumunta — Rundunar Soji
An umarci kwamandoji da shugabannin rundunoni da su koma sansanoninsu domin sake wayar da kan jami’ai kan illolin amfani da kafafen sada zumunta ba bisa ƙa’ida ba.
Rundunar Sojin Najeriya ta gargaɗi jami’anta kan amfani da kafafen sada zumunta, tana mai cewa duk wanda ya karya dokokin da suka shafi amfani da su zai fuskanci hukunci.
Babban jami’in kula da ladabtarwa na rundunar, Manjo Janar Mathias Erebulu ne ya bayyana hakan yayin wani taron horaswa ga jami’an soja masu aikin zartar da doka, kamar yadda tashar talabijin AIT ta ruwaito ranar Alhamis.
- Sojoji sun bindige ’yan ta’adda 3 a Zamfara
- Jami’an tsaro sun kama ɗan takarar Sanatan Taraba ta Tsakiya, Bello Boɗejo
Erebulu ya umarci kwamandoji da shugabannin rundunoni da su koma sansanoninsu domin sake wayar da kan jami’ai kan illolin amfani da kafafen sada zumunta ba bisa ƙa’ida ba.
“Sojojinmu ba su da abin yi a kafafen sada zumunta. Duk wanda ya karya dokar farko da ta shafi amfani da kafafen sada zumunta za a hukunta shi,” in ji shi.
Janar ɗin ya kuma tunatar da jami’an soja cewa kundin tsarin mulkin Najeriya bai ba su damar tsare fararen hula a sansanonin soja ba.
Ya ce duk wani farar hula da sojoji suka kama dole ne bayan gudanar da binciken farko a miƙa shi ga hukumar da ta dace cikin awa 24.
“Bisa tsarin mulki, bai kamata a riƙa tsare fararen hula a wurarenmu ba,” in ji shi.
Taron horaswar dai ya mayar da hankali ne kan inganta ladabtarwa da gudanar da aiki yadda ya kamata a tsakanin jami’an ’yan sandan soja.