Sojoji ba su da kayan aikin da za su iya tunkarar ’yan Boko Haram – Gwamna Gaidam
Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya roki Gwamnatin Tarayya ta kara yawan sojoji da kayan aiki na zamani domin karfafa kokarinsu na dakile hare-haren ’yan Boko Haram a jihar da sauran sassan kasar nan. Gwamnan ya bayyana haka ne bayan yya ziyarci wuraren da ake zargin ’yan Boko Haram da kai wa hari a […]

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya roki Gwamnatin Tarayya ta kara yawan sojoji da kayan aiki na zamani domin karfafa kokarinsu na dakile hare-haren ’yan Boko Haram a jihar da sauran sassan kasar nan.
Gwamnan ya bayyana haka ne bayan yya ziyarci wuraren da ake zargin ’yan Boko Haram da kai wa hari a ranar Alhamis din makon jiya a Damaturu fadar jihar, inda ya ce a yayin da jami’an tsaro ke bakin kokarinsu don kare jihar ga alama an shammace su a harin baya-bayan nan.
Ya fadi a wata sanarwa dauke da sa hannun Kakakinsa Abdullahi Bego cewa, “In da a ce muna da masu sintiri dare da rana da dabarun samun bayanai daga jami’an tsaronmu, da an dakile wasu daga cikin munanan hare-haren.”
Gwamnan ya yaba wa jami’an tsaron kan mayar da martani game da harin, inda ya bukaci su kara sadaukar da kai wajen kare rayuka da dukiya a jihar. Sai ya ba da sanarwar ba iyalan jami’an tsaron da aka kashe Naira miliyan daya kowannensu, yayin da za a tallafa wa wadanda suka samu rauni da rabin miliyan kowannensu domin su yi jinya.
Kwamandan Ayyuka na Musamman na Ruduna ta Uku Kanar Abdullahi da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Rufa’i Alkali sun yi bayanai ga Gwamnan kan artabun, inda suka ce an samu gawarwakin maharan sama da 30, kuma suka yi alkawarin ci gaba da sadaukar da kai don tabbatar da tsaro a jihar.
kazamin harin na makon jiya ya yi kama da wanda aka taba kai wa a ranar 4 ga Nuwamban shekara 2011 da ya halaka rayukan jama’a da na jami’an tsaro masu yawa a sassan garin Damaturu.
Majiyoyin da ke kusa da sassan da suka yi fama da harin sun shaida wa Aminiya cewa, maharan sun fara kai hare-haren ne da misalin karfe 5:30 na yamma, inda suka fara da bataliyar sojoji ta 233 da ke kauyen Kukareta daga nan suka kwararo zuwa Damaturu suka kai hari ga shingen duba motoci na kusa da NNPC Mega Station.
Wani mazaunin wurin ya shaida wa Aminiya cewa bayan da jami’an tsaron JTF suka tarwatsa maharan sai suka kwarari babban ofishin ’yan sandan kwantar da tarzoma da ke hanyar Gujba daga nan ne da kimanin karfe 8:00 na dare aka rika jin karar abubuwa masu fashewa a yankin da suka nufa.
Maharan sanye da kakin soja sun kone babban ofishi da gidan kwamnadan mopol da daga bisani suka zarce ofishin ’yan sanda na C. Dibision suka kone tare da wata motar ’yan sanda bayan sun kwashe makaman da ke wurin.
Majiyarmu ta ce maharan sun zarce zuwa babban ofishin CID shi suka jefa abubuwa masu fashewa, sannan suka zarce zuwa ofishin babban jami’in ’yan sandan yanki (Area Command) suka kone shi.
Wata majiya ta bayyana wa Aminiya cewa maharan sun je asibitin Sani Abacha da ke Damaturu suka dauki motocin daukar marasa lafiya guda biyu suka bude dakin adana magunguna na asibitin suka kwashi magunguna iya son ransu suka tafi.
Kakakin JTF a Jihar Yobe Kyaftin Eli Lazarus ya ce sun kashe akalla mahara 21 tare da damke masu yawa. Kuma sun kwato makaman da suka hada da bidigar AK47 guda 4 da makamin harbo jiragen sama 1 da bama-bamai masu yawa da harsasai 709 da motoci kirar Toyota Hilud guda uku da sauransu.