Sojoji da fasinjoji 64 sun mutu a harin ta’addanci a Mali

Wasu hare-hare da aka kai wa wani sansanin soji da kuma wani jirgin ruwan fasinjoji sun hallaka sojoji da fararen hula 64 a Mali.

Sojoji da fasinjoji 64 sun mutu a harin ta’addanci a Mali

Assimi Goita, Shugaban Rikon Kasar Mali

Sojoji da fararen hula 64 sun rasu a wasu hare-hare da aka kai wani sansanin soji da kuma jirgin ruwan fasinja a Arewacin kasar Mali.

Gwamnatin kasar Mali ta ce “alkaluma farko sun tabbatar da rasuwar fararen hula 15 da kuma sojoji 49” a hare-haren da aka kai a lokuta daban-daban ranar Alhamis.

Hukumomin kasar ba su fayyace adadin mutane da abin ya shafa a kowanne daga cikin hare-haren ba, amma ta ce masu ikirarin jihadi ne suka kai hare-haren.

Ta ce maharan sun kai wa sojojin farmaki ne a sansaninsu da ke Bamba, fararen hulan kuma an kai musu hari ne a wani jrgin ruwan fasinja da ke hanyarsa ta zuwa Tumbuktu a Kogin Niger aka hallaka su.

wani soja da ya bukaci kamfanin dillancin labarai na AFP ya boye sunansa ya ce an kai wa jirgin ruwan hari ne da rokoki, kuma sojoji na ci gaba da aikin ceto.

Turmutsutsun abinci: Najeriya na fuskantar annobar yunwa – LP

An yanke wa direba hukuncin kisa kan kashe mutum 35 a China

Lalacewar jirgin ƙasa ya sa fasinjoji sun maƙale a Delta

Jerin Manyan Dambarwan Kano a 2024