Sojoji da masu garkuwa da mutane sun yi musayar wuta
Sojoji sun yi artabu da masu garkuwa da mutane da suka sace matafiya a Karamar Hukumar Ikole ta Jihar Ekiti. Faruwar lamarin na ranar ranar Juma’a da misalin karfe 10 na safe ya sa matafiya kaurace wa babban titin da ya tashi daga Ayedun zuwa Ilasa-Ayebode na tsawon awanni. Matashi yana neman wanda zai saye […]
Sojoji sun yi artabu da masu garkuwa da mutane da suka sace matafiya a Karamar Hukumar Ikole ta Jihar Ekiti.
Faruwar lamarin na ranar ranar Juma’a da misalin karfe 10 na safe ya sa matafiya kaurace wa babban titin da ya tashi daga Ayedun zuwa Ilasa-Ayebode na tsawon awanni.
- Matashi yana neman wanda zai saye shi a Kano
- Ya sayar da kodarsa ya sayi wayar iPhone, daya kodar kuma ta daina aiki
Wani wanda ya tsallake rijiya da baya a hannun masu garkuwar ya ce sau biyu sojoji na fatattakar ’yan bindigar a yankin Ayebode da Ilasa zuwa cikin daji domin hana su sakat.
Ya ce wasu matafiya uku sun yi rashin sa’a a hanyar Ayedun-Ekiti zuwa Ilasa inda masu garkuwar da sojoji suka kora suka bude wa motarsu wuta suka tafi da mutum uku, sauran mutum biyu kuma suka tsere da raunukan harbi.
Bayan ’yan bindigar sun yi garkuwa da wasu matafiya ukun a yankin Ayedun Ekiti sojoji sun kara fatattakar su.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ekiti, ASP Sunday Abutu, ya tabbatar wa manema labarai cewa an yi garkuwa da mutum hudu.
Sai dai ya ce rundunar hadin gwiwar sojoji da ’yan sanda ta yi nasarar cafke mutum shida daga cikin ’yan bindigar.