Sojoji da ’yan banga sun kwato shanu 53 da aka sace a Suleja
• Wannan ne lokaci mafi muni a rayuwar makiyaya – Miyetti Allah ’Yan banga da suka samu tallafin sojoji a garin Suleja ta Jihar Neja, sun samu nasarar kwato shanu 53 daga hannun barayin shanu a daidai lokacin da suke yunkurin tserewa da su. Shanun dai an sato su ne a ranar Alhamis din makon […]
• Wannan ne lokaci mafi muni a rayuwar makiyaya – Miyetti Allah
’Yan banga da suka samu tallafin sojoji a garin Suleja ta Jihar Neja, sun samu nasarar kwato shanu 53 daga hannun barayin shanu a daidai lokacin da suke yunkurin tserewa da su. Shanun dai an sato su ne a ranar Alhamis din makon jiya a kauyen Fadamar-Abushi da ke wajen garin Suleja bayan barayin da aka ce adadinsu ya kai 20, sun yi wa kauyen kawanya da misalin karfe 2:00 na dare.
Wasu mazauna kauyen da suka zanta da wakilinmu sun ce bayan faruwar lamarin, an sanar da ’yan banga da sojoji a garin Suleja kuma ba su bata lokaci ba suka bi sawunsu daga burtalin shanu da ya tashi daga kauyen, suka cin musu a wani kauyen Lunda da ke kusa da garin Maje a kan hanyar zuwa Minna da misalin karfe 4:00 na dare.
Wani mai suna Abdulkarin Tashi ya shaida wa wakilinmu cewa, barayin shanun sun gudu tare da barin shanun bayan sun fahimci cewa ana bin su. Ya ce sai dai jami’an tsaron sun jinkirta kaiwa ga shanun har zuwa karfe 6:00 na safe, sannan suka dawo da su kauyen tare da masu shanun.
Wadanda suka zanta da wakilinmu sun ce harin shi ne na uku a cikin wata guda a kauyen, kuma sakamakon hakan makiyaya da dama sun yi hijira daga kauyen a ranar Juma’ar da ta gabata.
Da aka tuntubi, babban jami’in ’yan sanda na yankin Suleja ACP Abubakar Yahaya, ya ce labarin aukuwar lamarin bai kai gare shi ba.
A wani labarin kuma shugabannin Fulani makiyaya da suka hada da ardo-ardo da shugabannin kungiya, sun koka a kan matsalar satar shanu da kashe makiyaya da barayin ke yi, inda suka ce matsalar ce mafi muni a tarihin kasar nan ga jama’arsu.
Shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ta kasa Alhaji Muhammadu Kirowa Ardon Zuru ne ya bayyana haka a yayin taron da ardodi da shugabanninin kungiyar daga garuruwa daban-daban na kasar nan da ya gudana a ranar Litinin din makon jiya a Abuja.
Shugaban na Miyetti Allah wanda ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kawo karshen matsalar satar shanu, ya yi gargadin cewa jefa Bafulatani marar ilimi a matsayin mara aikin yi, hadarinsa ya dara na mara aikin yi da ya yi karatu.
Wani tsohon shugaban kungiyar ta kasa Alhaji Abba Kawu wanda ya ce adadin Fulani a kasar nan ya kai miliyan 26, ya ce abin takaici ne a ce Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da bukatunsu da sula hada da na tsaron lafiyar jama’a da na dabbobi.
A jawabin Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar wanda shi ne Shugaban Kwamitin Amintattu na kungiyar Miyetti Allah, alkawarin mika bukatun kungiyar ya yi ga Shugaban kasa Goodluck Jonathan, sai dai ya bayyana cewa bisa la’akari da yawansu, al’umman Fulani na iya kawo sauyin gwamnati a dukkan matakai idan suna ganin ba a damu da bukatunsu ba.
Sauran wadanda suka yi jawabi a wurin taron sun hada da wakilan Hukumar Ilimin Makiyaya (NCNE) da kungiyar Manoma ta kasa (ALFAN) da kungiyar Masu Fataucin Dabbobi da Abinci da sauransu wadanda suka ce matsalar ta shafe su.