Sojoji da ’yan sanda sun ba hammata iska a Enugu
An ba hammata iska a tsakanin ’yan sandan yaki da fashi da makami (SARS) da wasu sojojin Runduna ta 82 da ke Enugu a yankin Ibagwa-Nike na karamar Hukumar Enugu ta Gabas a Jihar Enugu, inda aka ce mutum daya ya salwanta.Mamacin wanda ba a tantace soja ne ko dan sanda ba, a yayin rikicin […]
An ba hammata iska a tsakanin ’yan sandan yaki da fashi da makami (SARS) da wasu sojojin Runduna ta 82 da ke Enugu a yankin Ibagwa-Nike na karamar Hukumar Enugu ta Gabas a Jihar Enugu, inda aka ce mutum daya ya salwanta.
Mamacin wanda ba a tantace soja ne ko dan sanda ba, a yayin rikicin zauna gari banza da ake kira eriya boys sun shiga cikin rikicin da ya jawo kone motar ’yan sandan da suka je kame da ita.
Kamar yadda Aminiya ta samu labari a kokarin kama wasu mutum bakwai da ake zargi da aikata laifi ne da ’yan sandan SARS suka yi rikicin ya barke.
Wata majiya ta ce rikicin ya samo asali ne a lokacin da ’yan sandan suka je kauyen Umuanekoda da ke Ibagwa-Nike don kama wasu da ake zargi da hannu wajen kama mutane ana garkuwa da su a yankin, sai wani mutum da ake zargi da kashe wani attajiri a wani kauye.
Majiyarmu ta ce kafin ’yan sandan su fara aikinsu sai da suka sanar da sojojin wadanda suke aiki a bakin kasuwarAbakpa, amma da ’yan sandan suka kama wadanda ake zargin su takwas suka ajiye su cikin motarsu kirar Hilud, an yi zargin sojojin sun hana a tafi da su, kuma suka harbe tayoyin motar ’yan sandan.
Wannan ne ya jawo fada ya barke tsakanin sojojin da ’yan sandan suka fara harbe-harbe a iska, lamarin da ya sa jama’a suka arce har da mutane takwas din da aka kama.
Wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’Yan sandan Jihar Enugu, Ebere Amaraizu game da lamarin, inda ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya kuma ce suna ci gaba da neman masu laifin da suka arce.