‘‘Sojoji ku daina musguna wa ma’aikatan Daily Trust’’
Kwamitin Kare ’Yan Jarida na Duniya (CPJ) ya bukaci mahukuntan Najeriya su daina musguna jaridar Daily Trust tare da kyale wakilanta su rika nemo labara cikin ’yanci.A ranar Alhamis din makon jiya ne sojoji suka auka wa ofishin Shiyyar Arewa maso Gabas na Daily Trust da ke Maiduguri, bayan da jaridar ta buga wani labari […]
Kwamitin Kare ’Yan Jarida na Duniya (CPJ) ya bukaci mahukuntan Najeriya su daina musguna jaridar Daily Trust tare da kyale wakilanta su rika nemo labara cikin ’yanci.
A ranar Alhamis din makon jiya ne sojoji suka auka wa ofishin Shiyyar Arewa maso Gabas na Daily Trust da ke Maiduguri, bayan da jaridar ta buga wani labari a ranar Laraba kan zargin sojojin sun ki bin umarnin su tafi don fuskantar mayakan Boko Haram, har sai an ba su ingantattun makamai, kamar yadda rahotanni suka nuna.
Babban Editan Jaridun Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Trust da Aminiya Malam Mannir dan-Ali, ya shaida wa CPJ cewa labarin mai kanun “Rikicin Boko Haram: Sojoji sun botsare kan rashin ingantattun makamai,” ya ginu ne kan tattaunawa da sojojin. Kuma gidan rediyon BBC ma ya ruwaito tawayen sojojin, wanda manyan sojoji suka ce suna bincike a kai.
Sojojin sun gayyaci manajojin jaridar biyu Jamilu Aliyu da Aminu Ado, suka tsare su a hedkwatar soja, inda suka shaida musu su daina sukar sojoji a jaridars, dan-Ali ya shaida wa CPJ. Bayan awa daya an saki jami’an biyu.
Sojojin sun fitar da wata sanarwa suna neman Daily Trust ta karyata labarin, kuma a gaba ta rika tuntubar hukumomin soja kan duk wani labara kan sojoji da tsaron kasa. “Kuma gaza yin haka, nag aba zai jawo daukar mataki,” inji sanarwar. Sai dai ba a fadi irin matakin da za a dauka ba. Kuma Malam Mannir dan-Ali ya shaida wa CPJ, cewa jaridar tana nan kan labarinta kuma ba za ta karyata labarin ba.
Kakakin Hedkwatar Tsaro Manjo Janar Chris Olukolade, ya shaida wa CPJ cewa babu “Wani mataki da ake shirin dauka kan Daily Trust ko kowane gidan jarida.”
Shugaban Nahiyar Afirka na Kwamitin CPJ, Peter Nkanga ya ce: “Wajibi ne sojojin Najeriya su daina musguna wa Daily Trust da sauran jaridu masu zaman kansu.” Ya kara da cewa: “Jama’ar Najriya sun cancanci samun nau’o’in bayanai, kuma ’yan jarida suna da damar gudanar da aiki ba tare da tsoron daukar fansa ba.”
A ’yan watannin nan sojojin Najeriya sun rika musguna wa jaridu masu zaman kansu, ciki har da Daily Trust kan labaran da suke bayarwa a cewar binciken CPJ. A watan Yuni a wani tsararren shiri, sojoji da jami’an tsaro na farin kaya sun kawo cikas ga rarraba jaridu da dama ciki har da Leadership da Daily Trust da The Nation da kuma Punch.