Sojoji ku kokarta ’yantar da al’umma daga mahara —Shehun Borno
Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar- Ibn Garbai Al-Amin El-Kanemi, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da sojojin Najeriya da su ci gaba da ƙoƙartawa wajen kakkaɓe ragowar ’yan Boko Haram. Musamman wadanda ke ci gaba da mamaye hedikwatar Karamar Hukumar Guzamala da sauran al’ummomi a Kukawa da ke ƙaramar hukumar Abadam. A cewar […]
Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar- Ibn Garbai Al-Amin El-Kanemi, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da sojojin Najeriya da su ci gaba da ƙoƙartawa wajen kakkaɓe ragowar ’yan Boko Haram.
Musamman wadanda ke ci gaba da mamaye hedikwatar Karamar Hukumar Guzamala da sauran al’ummomi a Kukawa da ke ƙaramar hukumar Abadam.
A cewar Mai Martaba Shehun na Borno, ya kamata miliyoyin mutanen da suka rasa matsugunansu su koma gidajen kakanninsu don yin rayuwa ta yau da kullun da suka haɗa da noma da kamun kifi don ciyar da kansu.
Ya ce hanya ɗaya tilo da za a maido da waɗannan yankuna a cikin al’ummomin da abin ya shafa ita ce sojoji da sauran jami’an tsaro su sa himma da gaske wajen yaƙi da ‘yan ta’addan da yankunan ke ƙarƙashin ikonsu musamman a Karamar Hukumar Guzamala, inda babu farar hula da ke da cikakkiyar rayuwa a yankin na shekaru masu yawa.
- Yadda aka gudanar da bikin Sallah a Masarautar Fika a Yobe
- Kano: APC ta buƙaci a kama Kwankwaso kan kalaman da ya yi
Mai martaba Shehun na Borno ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai wa muƙaddashin gwamnan Borno, Dokta Umar Kadafur gaisuwar Sallah a gidan gwamnati da ke Maiduguri.
A makon da ya gabata ma dai Shugaban majalisar dokokin jihar Borno, Abdulkarim Lawan, a lokacin da yake gabatar da saƙon fatan alheri a wajen bikin Ranar Dimokuradiyya, ya bayyana makamanciyar wannan kira game da yankin na ƙaramar hukumar Guzamala.
Shehun ya kuma yaba da irin sadaukarwar da sojojin Najeriya suka yi wajen dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas, da ma kasa baki daya.
Ya ƙara da cewar, abin ban takaici ne irin yadda wadannan ’yan tada kayar baya suke hana iyaye da ’ya’yansu samun filayen noma, ko samun ingantaccen ilimi, wanda a cewarsa yana da haɗari ga bil’adama da kuma ci gaba mai ɗorewa.