Sojoji na ci gaba da samun nasara a kan Boko Haram
Rundunar Sojin Najeriya ta Bakwai ta samu nasarar kubutar da mutum 178 da suka hada da mata da yara da kuma tsofaffi, da suke hannun ’yan Boko Haram na tsawon lokaci a wasu kauyukan karamar Hukumar Bama da ke Jihar Borno.Rundunar ta ce ta kuma samu nasarar lalata akasarin sansanonin ’yan Boko Haram da dama […]
Rundunar Sojin Najeriya ta Bakwai ta samu nasarar kubutar da mutum 178 da suka hada da mata da yara da kuma tsofaffi, da suke hannun ’yan Boko Haram na tsawon lokaci a wasu kauyukan karamar Hukumar Bama da ke Jihar Borno.
Rundunar ta ce ta kuma samu nasarar lalata akasarin sansanonin ’yan Boko Haram da dama a samamen da ta kai zuwa wuraren, a karkashin shirinta na “Zaman Lafiya Dole” da ta kaddamar don yakar ayyyukan ta’addanci.
Kakakin Rundunar Kanar Tukur Gusau, ya ce daga cikin mutanen da suka kubutar akwai yara 101 da mata 67 da tsofaffin maza 10 daga sansanonin ’yan ta’addan a kauyukan Fadan da Aulari da Shuwarin da Wulari da Ngoro Dauye da Jidori da Alikashiri da Kalzamari da Shuwari da kuma Kalzamari Kanuri.
Ya ce rundunar ta kama wani babban kwamandan Boko Haram da yanzu haka ake yi masa tambayoyi, tare da gano ababen hawa biyar da tutocinsu uku.