Sojoji na tsare da ’yan Boko Haram 5000 – Buratai
Babban Hafsan Sojin Kasa Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce akalla mutum 5,475 da ake zargin’ yan Boko Haram ne suke tsare a hannun sojoji, inda ya ce kuma an kashe dubban ’ya’yan kungiyar. Janar Burutai yana magana ce a wajen taron shekara-shekara da bayar da lambobin yabo karo na 16 na Kungiyar Sanya Ido […]
Babban Hafsan Sojin Kasa Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce akalla mutum 5,475 da ake zargin’ yan Boko Haram ne suke tsare a hannun sojoji, inda ya ce kuma an kashe dubban ’ya’yan kungiyar.
Janar Burutai yana magana ce a wajen taron shekara-shekara da bayar da lambobin yabo karo na 16 na Kungiyar Sanya Ido kan Tsaro ta Afirka da aka gudanar a Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.
Babban Hafsan Sojin Kasa wanda Babban Jami’in Tsare-Tsare da Shirye-Shirye na Rundunar Sojin Najeriya Laftana Janar Lamidi Adeosun ya wakilta, ya ce sojoji sun lalata wuraren hada bama-bama na ’yan ta’addan har guda 32.
Ya ce adadin ’yan ta’addan ya yi matukar raguwa daga dubu 35 da aka kiyasta zuwa kasa da dubu biyar, inda ya ce sojoji sun riga sun samu nasara a yakin.
Da yake gabatar da jawabin budew taron mai taken: “Rawar Sojojin Najeriya Wajen Magance Matsalar Tsaron Cikin gida da Farmaki daga Waje a Najeriya: Darussa daga Duniya da Kuma Mafita,” Janar Buratai ya ce, an kashe dubban ’yan ta’addan, kuma an kama 5,475, tare da lalata wuraren hada bama-bamansu 32. Kari a kan haka yawan ’yan Boko Haram ya ragu sosai zuwa kasa da 5000 daga dubu 35 da ake kiyasin sun kai a baya,” inji shi.
Sai dai ya ce, “A bangaren sojojin su ma sun rasa hafsoshi da jami’ansu a kokarin magance matsalar tsaron da ke barazana ga kasar nan. Hakika ta hanyar kokarin Sojin Najeriya muna samun nasara a yaki da Boko Haram.”
Janar Buratai ya ce kididdiga daga Hukumar Bayar da Tallafin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta nuna Boko Haram ta kashe mutum dubu 30 zuwa dubu 100 tare da raba mutane sama da miliyan biyu da gidajensu inda a yanzu haka suke zaman gudun hijira a sansanoni ’yan gudun hijira 35.
Ya bukaci a kara samun karfin hali daga bangaren shugabanni da manyan kasa wajen yaki da ta’addanci wanda ya ce hakan ya kunshi ‘yunkuri na gaba daya’ daga gwamnati wanda ya kunshi bangaren zartarwa da majalisa da na shari’a. Ya ce irin wannan Amurka ta nuna a tsawon shekara goma da ta yi tana farautar Osama bin Laden.