‘Sojoji na yi wa rayuwata barazana a Gombe’
Sakataren Jin dadi da Walwala na Jam’iyyar APC reshen Jihar Gombe, Muhammad Sunusi Ataka, ya yi zargin cewa an tura sojoji suna yi wa rayuwarsa barazana. Sakataren ya ce yana tsaye a kofar gidansa a ranar Juma’ar da ta gabata dauke da ’yarsa a hannu shi da wani abokinsa Usman Mahmud, Ma’aikaci a Kwalejin Ilimi […]
Sakataren Jin dadi da Walwala na Jam’iyyar APC reshen Jihar Gombe, Muhammad Sunusi Ataka, ya yi zargin cewa an tura sojoji suna yi wa rayuwarsa barazana.
Sakataren ya ce yana tsaye a kofar gidansa a ranar Juma’ar da ta gabata dauke da ’yarsa a hannu shi da wani abokinsa Usman Mahmud, Ma’aikaci a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE (T) da ke Gombe, sai ya ga sojoji da bindigogi sun dira daga kan motarsu sun cukuikuye masa wando suna dukansa suna ce su shiga gidansa.
Ya ce sai suka shiga gidan suka warwargaza komi, har cikin ban-daki sun caje, ba wurin da ba su shiga ba, bayan sun zaunar da shi.
Sunusi Ataka, ya ce bayan sun bincike gidan ne suka ce masa sun samu labarin ya gina gida a cikin watan biyar, kuma sun samu labarin ya yi tafiya ina ya je, ya ce musu ya je Maiduguri ne. Suka sake cewa me ya je yi, ya ce ya je neman aure kuma zai koma ranar Litinin.
Ya ce sun tambaye shi motocinsa nawa ne, kuma an ce wani mutum ya mutu a gidansa me ya kashe shi, ya ce babu wanda ya mutu a gidansa. Ya ce, sun fi minti ashirin suna yi masa tambayoyi a karshe suka shiga motocinsu suka tafi.
dan siyasar ya ce wannan ba shi ne karo na farko da aka fara yi masa barazana ba, domin a ranar zaben gwamnoni ma an tsare gidansa babu wata takarda ta nuna an zo a caje gidansa ko ana zarginsa da wani laifi, kuma ana yi masa haka ne saboda shi dan Jam’iyyar APC ne.
Ya zargi wani makwabcinsa Alhaji Gidado mai rikon Darakta a Ma’aikatar kasa da Safiyo da shirya masa wannan bita-da-kulli, inda ya ce dansa ya taba tare shi ya ce masa sai sun wulakanta shi, kuma kwana uku sai hakan ta faru. “Abin da ya hada ni da su shi ne na yi gini har ya kai linta suka ce sai na bar kafa uku, kuma saboda gudun rikici, mahaifina ya ce in cire kafa ukun, na rushe ginin gaba daya na sake bin yadda suke so, amma ba su rabu da ni ba,” inji shi.
Ya ce bai san me sojojin suka bari a cikin gidansa ba, domin ba tare da shi suka zaga ba, kuma har suka tafi ba su ce ga abin da suke zarginsa a kai ba.
Ya ce yana so uwar jam’iyyarsa ta APC ta san halin da ake ciki ne kafin daukar matakin doka a gaba.
Da wakilinmu ya tuntubi makwabcinsa Muhammad Gidado, dansa mai suna Abubakar Gidado, ya ce ba su da masaniya a kan abin da ya sa sojoji suka zo gidansa.
Abubakar Gidado, ya ce a kwana biyu da sojojin suka zo bincike a gidansa su ma hankalinsu bai kwanta ba, amma an rika yada jita-jitar samun gawar yara biyu a motarsa, sannan yawan zuwansa Maiduguri da yadda cikin kankanen lokaci ya tayar da ginin gidan sama, kila shi ya sa sojojin ke zargin ko dan Boko Haram ne. Ya ce ba su makwabtakar katanga da shi da gidan marigayi Yariman Gini Domaiy ne ya hada katanga, kuma shi da Sunusi ’yan uwa ne mahaifiyarsa yayar Sunusi ce.