Sojoji sun bindige ’yan mata ’yan uwan juna a kasuwa a Kaduna

Bindige ’yan matan da sojojin suka yi a cikin kasuwar ya sa mutane gudun famfalaki a garin Kidanda

Sojoji sun bindige ’yan mata ’yan uwan juna a kasuwa a Kaduna

Wasu sojoji sun dirka wa wasu ’yan mata biyu ’yan uwan juna harbi har lahira a bainar jama’a a wata kasuwa a Jihar Kaduna.

Ganau sun ce bindige ’yan matan da sojojin suka yi a cikin kasuwar ya sa mutane gudun famfalaki a garin Kidanda da ke ke Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.

Mutanen garin sun ce sojojin na wucewa a cikin motocinsu a kasuwar ne suka hango wasu mutane a kan babura, nan take suka kalubalance su.

Ana cikin haka ne sojojin suka bude wuta, su kuma  mutanen gari da suka ji karar harbe-harbe, kafin kiftawa da Bismilla suka ce kafa me na ci ban ba ki domin su tsira da rayukansu.

A garin guje-gujen ne harsashin sojojin ya sami wata budurwa mai suna Nurayn, mai shekara 16 da kanwarta, Khadija mai shekara 11, a yayin da suke kokarin tserewa bayan sojojin sun bude wuta.

Dan uwan ’yan matan, Salisu Shuaibu Kidanda, ya ce kannen nasa sun rasu ne sakamakon harbin da sojojin suka yi cikin jama’a.

“Idan ma Fulanin suke nufin harbi, to me zai sa su yi harbi zuwa cikin jama’a? Kannena na kokarin tserewa su koma gida ne harsasan suka same su, saboda a wajen kauyenmu kasuwar take.

“Har yanzu ko zuwa domin jajanta wa iyayenmu sojojin ba su yi ba, ’yan sanda ne kawai ne suka je. Muna neman a yi mana adalci a bi mana hakkinmu, babu dalilin da sai sa a kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, a tafi a bar su,” inji shi.

Shi ma wani mazaunin kauyen na Kidanda, ya ce bai kamata sojojin su yi harbi a kan jama’a ba saboda a lokacin, Fulanin da suke so su harba sun riga sun tsere zuwa daji.

Wakilinmu ya nemi karin bayani daga wurin sojoji, ya kuma tuntubi Mataimaikin Kakakin Rundana ta 1 ta Sojin Kasa ta Najeriya da ke Kaduna, Kanar Ezindu Idimah.

Amma Kanar Idimah ya bayyana mishi cewa an sauya mishi wurin aiki zuwa Abuja, sai dai ya wakilin namu da ya tuntubi wani mai suna Laftana Shehu; Har aka kammala  hada wannan rahoton ba a sami shi Laftana Shehun ba.