Sojoji sun bude wa Kwamandan Runduna ta Bakwai wuta a Maiduguri
Kwamandan Rundunar Sojoji ta Bakwai da ke Maiduguri, Manjo Janar Abubakar Muhammad, ya tsallake rijiya da baya a lokacin da wasu kananan sojoji suka kai wa jerin gwanon motocinsa hari a kan hanyarsa ta zuwa barikin soja na Maimalari da ke wajen garin Maiduguri, a shekaranjiya Laraba.Harin dai ya biyo bayan fusata ce da aka […]

Kwamandan Rundunar Sojoji ta Bakwai da ke Maiduguri, Manjo Janar Abubakar Muhammad, ya tsallake rijiya da baya a lokacin da wasu kananan sojoji suka kai wa jerin gwanon motocinsa hari a kan hanyarsa ta zuwa barikin soja na Maimalari da ke wajen garin Maiduguri, a shekaranjiya Laraba.
Harin dai ya biyo bayan fusata ce da aka ce sojojin sun yi, sakamakon kwanton baunar da ’yan bidiga suka yi wa abokan aikinsu suka kashe su a kan hanyarsu ta dawowa daga karamar Hukumar Kala-Balge a sanadiyyar umarnin da aka ba su na su dawo Maiduguri cikin dare. An ce an jibge gawarwakin wadannan sojoji a wani wuri da sauran ’yan uwansu suka rika ganinsu, inda hankalinsu ya tashi suka fusata tare da zargin manyan sojoji da danne musu hakkoki kuma suna sa ana kashe su.
Wata majiya ta tabbatar da cewa harbin bai kai ga kwamandan ba, amma ya lalata motarsa da wasu motocin, kuma bayanai sun ce kwamandan ya je asibiti domin a duba lafiyarsa.
A ’yan watannin nan hare-haren ’yan bindiga sun yi kamari a wasu yankunan kananan hukumomin Jihar Borno, musamman yankunan Arewa da Kudancin jihar, inda a ranar Talatar da ta gabata ’yan bindiga suka kai hari a karamar Hukumar Kala-Balge, inda daga nan ne sojojin da aka kashe suka fito.
To, amma Daraktan Labarai na Hedikwatar Tsaro da ke Abuja, Manjo Janar Chris Olukolade, ya fadi, a wata sanarwar da aka tura wa manema labarai ta hanyar sadarwa ta yanar gizo a garin Maiduguri, cewa wannan rikici ne na cikin gida kuma an riga an sulhunta.
Ba tun yau ba dai, kananan sojoji a garin Maiduguri ke zargin manyan sojojin da danne musu hakkokinsu a lokacin da suke fagen yaki da ’yan kungiyar Boko Haram a yayin da manyan ke cikin ofishinsu ba su san abin da ke faruwa da su ba.