Sojoji sun cafke masu safarar makamai a Filato
Daga cikin makaman da suka ƙwato akwai bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu da alburusai.
Dakarun Rundunar Operation Safe Heaven, da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Jihar Filato da wasu sassan Bauchi da Kaduna, sun kama riƙaƙƙun masu safarar makamai a yankin Naraguta da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.
Da yake magana da manema labarai a ranar Talata a Jos, mai magana da yawun rundunar, Manjo Stephen Zhakom, ya ce sojojin sun kuma gano makamai da alburusai masu tarin yawa yayin da suka kai samame.
- Gwammoni sun ciyo bashin N446bn duk da karuwar kudaden FAAC
- Majalisar Wakilai ta ba waɗanda Ambaliyar Maiduguri ta shafa 100m
Manjo Zhakom ya ce, “Sojojin sun kama wasu ƙasurguman masu safarar bindigogi guda biyar tare da gano makamai da alburusai a yayin wani samamen sirri da aka kai Jihar Filato.
Ya ƙara da cewa, “An gudanar da samamen ne tsakanin ranar 16 zuwa safiyar ranar 17 ga watan Satumba.
Kazalika, ya ce dakarun sun yi wa sansanin mai suna Mohammed Sani ƙawanya a yankin da ake haƙar ma’adinai na Naraguta, kusa da hanyar Bauchi a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.
“A yayin samamen, sojojin sun kama wanda ake zargi da safarar bindigogi tare da wasu mutum huɗu, sannan sun gano makamai daban-daban ciki har da bindigogi AK-47 guda biyu,” in ji shi.