Sojoji sun cafke shugaban ’yan bindiga a Zamfara
Sojojin sun kama shi ne bayan ya je cin kasuwar mako
Dakarun Sojin Najeriya, sun kama Kachalla Halilu wanda ake zargin ɗaya daga cikin shugabannin ’yan bindiga ne a Jihar Zamfara.
Rahotanni sun ce sojojin sun kama shi ne a wata kasuwar mako-mako da ke garin Shinkafi, bayan sun samu sahihan bayanan sirri game da inda yake.
- Masu kai wa Boko Haram bayanai sun shiga hannu a Yobe
- Sai da muka haƙa rijiyoyi sama da 30 don samun ruwa a Masallacin Ilori —Kwamiti
Majiyoyi sun bayyana cewa dakarun rundunar sojin yankin sun kai samame cikin gaggawa zuwa kasuwar, inda suka yi nasarar cafke wanda ake zargin ba tare da wata matsala ba.
An kuma gano wasu kayayyaki a wajensa da suka haɗa da babur, wayar salula, hula da kuma wasu magungunan dabbobi.
Wata majiya ta ce nasarar kamen ta samu ne saboda yadda sojojin suka yi aiki da bayanan sirrin da suka samu cikin gaggawa.
Bayan kama shi, an miƙa wanda ake zargin ga jami’an leƙen asiri domin ci gaba da bincike da gano irin rawar da ya taka a hare-haren ’yan bindiga a yankin.
Kamen na daga cikin ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi domin kawo ƙarshen ayyukan ’yan bindiga da sauran masu tayar da ƙayar baya a Zamfara da sauran jihohin Arewa maso Yamma.
Jami’an tsaro sun ce binciken da ake yi zai taimaka wajen gano ƙarin bayanai kan ayyukan ta’addanci da wanda ake zargin ke da hannu a ciki.