Sojoji sun ceto fasto da matarsa da aka sace a Filato

Rundunar ta jaddada ƙudirinta na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Sojoji sun ceto fasto da matarsa da aka sace a Filato

Sojojin Rundunar Operation Enduring Peace sun ceto wani fasto da matarsa daga hannun masu garkuwa da mutane a ƙauyen Faggem da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos a Jihar Filato.

Mai magana da yawun rundunar, Kyaftin Polycarp Oteh ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi cewa ma’auratan sun samu raunuka yayin da suke tsare a hannun maharan.

A cewarsa, sojojin sun samu kiran gaggawa daga ƙauyen Faggem a ranar 5 ga watan Yuni, 2026, kan yunƙurin sace mutane da aka yi.

Nan take suka garzaya wajen tare da tilasta wa masu laifin tserewa zuwa wani daji da ke kusa da yankin.

Yayin gudanar da aikin, sojojin sun samu nasarar ceto faston da matarsa daga hannun maharan.

Daga bisani an garzaya da su zuwa asibitin Bokkos domin samun kulawar likitoci.

Haka kuma jami’an tsaro sun fara farautar waɗanda suka tsere.

A wani labarin a Jihar Kaduna, sojojin sun ceto mutum biyu da ’yan bindiga suka sace a yankin Rafin Tagwai da ke Ƙaramar Hukumar Sanga.

Kyaftin Oteh, ya ce sojojin sun kai ɗauki ne bayan samun rahoton cewa wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne sun tare hanya tsakanin Rafin Tagwai da Angwan Dariya da sanyin safiyar ranar Asabar.

Da isarsu wajen, sun gano cewa maharan sun yi garkuwa da wasu fasinjoji da ke tafiya a cikin motar haya.

Sojojin sun ƙwato ƙwanson harsasai takwas na bindiga, sannan sun bi sahun maharan zuwa cikin daji domin ceto waɗanda aka sace.

Wannan sintiri ya yi nasarar kai ga ceto fasinjoji biyu da suka samu raunuka.

An kai su asibiti a Fadan Karshi domin samun kulawa, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.

Kyaftin Oteh, ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar sojin za ta ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro domin kawar da masu aikata laifuka da tabbatar da zaman lafiya.