Sojoji sun ceto ma’aikaciyar agaji daga hannun ISWAP bayan shekara 4

Sojojin Najeriya sun ceto wata ma’aikaciyar agaji Grace Taku, bayan ta ta shafe shekara hudu a hannun mayakan kungiyar ISWAP.

Sojoji sun ceto ma’aikaciyar agaji daga hannun ISWAP bayan shekara 4

Sojojin Najeriya sun ceto wata ma’aikaciyar agaji Grace Taku, bayan ta ta shafe shekara hudu a hannun mayakan kungiyar ISWAP.

A safiyar Asabar wata majiyar tsaro ta shaida mana cewa ana duba lafiyar Grace a asibitin sojoji na Maimalari da ke Maiduguri, bayan an ceto ta.

Majiyar ta ce sojojin sun “An ceto ta a galabaice, amma cikin hankalinta,” a wani samame a maboyar mayakan ISWAP.

Grace, ma’aikaciyar kungiar agaji ta Action Against Hunger (ACH)ce, kuma wata abokiyar aikinta ta tabbatar wa wakilinmu cewa sun kai mata ziyara a asibitin sojojin.

Jami’ar ta ce,  “Mun ji dadin ganin ta bayan shekara uku da wata 10 a hannun ISWAP. Na yi kuka sosai da na gan ta. Allah mai iko!

“Mun samu labari cewa sojoji sun ceto ne a 13 ga watan Mayu, 2023, Allah Ya saka wa sojojin rundunar Operation Hadin Kai da alheri.”

Wata majiyar ta ce kungiyar ISWAP ta sayar da Grace a matsayin baiwa, bayan rashin daidaitawa a tattaunawar kungiyar da Gwamnatin Tarayya a 2021.

A watan Yulin 2019 ne mayakan ISWAP suka yi garkuwa da Grace Taku da abokan aikinta biyar a yankin Damasak na Jihar Borno.

Kungiyar ta kashe sauran ta abokan aikin Grace su biyar, domin nuna fushinsu kan rashin samun biyan bukatunta daga gwamnati da jami’an tsaro.