Sojoji sun ceto malamin Jami’a da aka sace a Taraba

Rundunar ta nemi haɗin kan jama’a wajen bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a jihar.

Sojoji sun ceto malamin Jami’a da aka sace a Taraba

Rundunar Sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar jami’an Hukumar DSS sun ceto Injiniya Joshua Saleh, wani malami a Jami’ar Taraba, wanda ’yan bindiga suka sace.

An sace malamin ne a ranar 31 ga watan Yuli, 2025, a hanyar Chinkai–Kente zuwa Wukari, da ke Ƙaramar Hukumar Wukari a Jihar Taraba.

Bayan samun sahihan bayanai, sojoji da DSS suka fara bincike tare da ƙoƙarin ceto shi a wurare da dama, ciki har da Kente, Sondi 1 da 2, Yaku, da Warawa.

A cewar Laftanar Umar Muhammed, mai magana da yawun rundunar, sojojin sun yi arangama da ’yan bindigar, inda suka yi musayar wuta.

’Yan bindigar sun gaza jure ruwan wutar da sojoji suka musu, wanda hakan ya sa suka tsere suka bar malamin.

Kwamandan Runduna ta 6, Brigediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba wa sojojin bisa ƙwarewar da suka nuna da kuma yadda suka haɗa kai da sauran jami’an tsaro wajen ceto malamin.

Janar Uwa, ya tabbatar wa jama’a cewa sojojin Najeriya za su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi da tabbatar da zaman lafiya a Jihar Taraba.

Ya kuma roƙi jama’a da su kasance masu lura tare da bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen yaƙi da miyagun laifuka.