Sojoji Sun Ceto Mata Da Yara 34 Daga Hannun Boko Haram a Borno
Mayakan kungiyar ISWAP uku sun mika wuya ga dakarun soji
A wani jerin hare-haren da rundunar hadin gwiwa ta MNJTF ta kai wa ’yan ta’adda, dakarun Operation Lake Sanity 2 sun yi nasarar kubutar da mata da kananan yara 34 daga hannun ’yan ta’addan Boko Haram.
Sojojin sun kuma hallaka wani dan ta’adda a a yayin hare-haren a kauyukan Mazuri, Itsari, Mudu, da Maleri da ke Kudancin Tafkin Chadi a Najeriya a ranar 15 ga Yuni 2024.
Hakazalika a ranar 17 ga watan Yunin 2024, mayaka uku daga kungiyar ISWAP da ke da sansani a tsibirin Jabilaram a tafkin Chadi sun mika wuya ga dakarun sa-kai na Wulgo.
Mayakan da aka bayyana sunayensu da Babakura Abubakar mai shekaru 20 da Abacha Kyari mai shekaru 28 da kuma Mohammad Adam mai shekaru 29, ya zuwa yanzu ana ci gaba da yi musu tambayoyi domin daukar mataki na gaba.
- An samu ƙaruwar rashin tsaro a Najeriya — Rahoto
- NAJERIYA A YAU: Shin Shawarar Buhari Ta A Koma Gona Za Ta Kawo Saukin Abinci?
Haka kuma, hare-haren da jiragen soji ke kaiwa da nufin kakkabe ayyukan ta’addanci a fadin yankin Tafkin Chadi, sun lalata motocin ’yan ta’addan guda uku da ke shirin kai wani babban hari a ranar 9 ga Yuni 2024 a yankin Kollaram.
Majiyar Zagazola Makama, kwararren masanin harkokin tsaron nan a Tafkin Chadi, ta jaddada cewar ayyukan kai hare-haren da ake yi ta ƙasa da ta sama na rage ƙarfin ƙungiyoyin ta’addanci a yankin.
Rundunar hadin gwiwar MNJTF na ci gaba da jajircewa wajen ganin an kawar da ta’addanci, da tabbatar da tsaron fararen hula, da kuma samar da yanayi mai aminci da zai tabbatar da dorewar zaman lafiya a yankin Tafkin Chadi da sauran yankunan da ke fuskantar hare-haren Boko Haram da ISWAP.
Kwamandan rundunar, Manjo Janar Ibrahim Sallau Ali, ya yaba wa kokarin sojojin tare da jaddada aniyar rundunar ta maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a illahirin yankin.