Sojoji sun ceto mata da yara 57 a Dajin Sambisa

Sojojin sun kashe ’yan ta’addan shida yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Sojoji sun ceto mata da yara 57 a Dajin Sambisa

Sojojin rundunar Operation Lake Sanity III da na Operation Haɗin Kai sun ceto wasu mutum 57 bayan kashe ‘yan ta’addan Boko Haram shida a Dajin Sambisa.

Bayanai sun ce sojojin tare da haɗin gwiwar wasu sojoji na musamman da ake kira Hybrid Force da kuma dakarun haɗin gwiwa na CJTF ne suka yi wannan aikin a yayin wani sintiri na yaƙi da ’yan ta’addar Boko Haram a Ƙaramar Hukumar Bama ta Jihar Borno.

Majiyoyin leken asiri sun shaida wa ƙwararren masani kan yaƙi da tayar da ƙayar baya a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama cewa, sojojin sun kai farmakin ne a ranar 12 ga watan Yulin 2024.

Majiyar Zagazola ta ce wannan farmakin ne ya yi sanadiyyar kashe ‘yan ta’addan shida, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Daga cikin mutane 57 da sojojin suka ceto sun haɗa da mata 20 da ƙananan yara 37.

Haka kuma, an gano wata babbar bindiga guda ɗaya, yayin da sojojin suka lalata duk wasu gine-ginen da ’yan ta’addan ke laɓewa a ciki.

NCC ta amince wa kamfanonin sadarwa ƙara kuɗin kira da data

Amurka jinsin mace da namiji kaɗai ta sani a hukumance — Trump

An rantsar da Donald Trump a matsayin Shugaban Amurka na 47

Za mu yi gwanjon motoci 891 da muka ƙwace — EFCC