An Ceto Matar Auren Da Boko Haram ta Sace Shekara 11 Da Suka Wuce

Sojoji sun ceto wata uwa da ’ya’yanta mata uku wadda Boko Haram ta yi wa auren dole dan kungiyar

An Ceto Matar Auren Da Boko Haram ta Sace Shekara 11 Da Suka Wuce

Sojojin Najeriya da hadin gwiwar rundunar farar hula CJTF sun kubutar da iyalan ’yan Boko Haram hudu, bayan sun yi musu kwanton bauna a kan hanyar Yuwe zuwa Komala a Karamar Hukumar Bama a Jihar Borno.

Wata majiyar leken asiri ta shaida wa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tayar da kayar baya, kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, cewa sojojin sun yi kicibis da iyalan Boko Haram ne a yayin da suke sintirin yaki da ta’addanci a Yuwe, inda suka yi musayar wuta.

Majiyar ta ce sojojin sun yi nasarar fatattakar ’yan ta’addan, inda suka yi watsi da iyalansu da makamansu.

Majiyar ta ce iyalan ’yan ta’addan da aka ceto sun hada da wata uwa mai shekara 24 ’ya’yanta mata uku, masu shekaru 2 da shida da kuma shekara 8.

Binciken farko ya nuna cewa an yi garkuwa da matar ce a lokacin da Boko Haram ta kai hari gidanta da ke kauyen Hantsa a gundumar Gulak a Karamar Hukumar Madagali ta jihar Adamawa a shekarar 2014.

An kai ta sansanin Njimiya na Boko Haram da ke dajin Sambisa inda aka yi mata auren dole da wani dan kungiyar da ta haifar wa ’ya’ya uku.

Majiyar ta ce a yanzu haka an mika iyalan da aka ceto a hannun sojoji domin yin bincike da kuma daukar matakin da ya dace a kai.